Shugaba Bola Tinubu ya umarci dukkan jakadun Najeriya a ƙasashen waje su dawo gida.
A wani ƙarin haske da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar ya yi, ya ce Tinubu ne ya umarce shi da ya maido dukkan jakadun gida.
Haka wata sanarwa ta bayyana, wadda Mashawarcin Ministan Harkokin Waje kan Yaɗa Labarai, Alkasim Abdulƙadir ya fitar, ɗauke da sa hannun sa a ranar Asabar.
Tun a ranar Alhamis ce Tinubu ya yi wa Jakadan Najeriya a Birtaniya kiranye, ba tare da bada dalili ko dalilan yin hakan ba.
Sanarwar da Abdulƙadir ya fitar na ɗauke da cewa shi dama kowane jakada Shugaban Ƙasa ne ke da ikon naɗa wanda duk ya ga dama, ko dawo da kowane ya ga dama.
Wannan kiranye da aka yi masu na nuni da cewa ba da daɗewa ba Tinubu zai sake naɗa wasu sabbi, wasu kuma a yi masu sauyin wuraren aiki.
Cikin wata sanarwa daban kuma, Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ya ce kiranyen da Tinubu ya yi wa jakadun, na da nasaba da sake nazarin harkokin ofisoshin jakadanci na faɗin duniya.
Sai dai kuma wata sanarwar ta ce Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York da wanda ke ofishin ta na Geneva, za su ci gaba da zama, har sai bayan kammala taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a ƙarshen watan Satumba ɗin nan.
Discussion about this post