Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Cikin Gida ta Ƙasa (FIRS), ta bayyana cewa a cikin shekarar 2022 ta tara wa Gwamnatin Tarayya Naira tiriliyan 10.18.
Haka kuma ta ce hukumar ta ɗaga ƙafa da kuma bayar da alfarmar ɗauke kuɗin haraji, wanda adadin sa zai kai har naira tiriliyan 1.81, duk a cikin 2022.
Rahoton da hukumar ya fitar na 2022 ne ya bayyana haka.
Rahoton ya nuna an ɗaga ƙafar yafe karɓar haraji domin a tallafa wa masu hada-hada da kasuwanci bunƙasa harkokin su.
FIRS ya ce cikin 2022 ya karɓi harajin naira tiriliyan 10. A cikin kuɗaɗen an karɓi Naira tiriliyan 4.2 daga ɓangarorin mai, sai kuma Naira tiriliyan a matsayin kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma rahoton ya nuna cewa FIRS ba ta cika alƙawarin ta ba, saboda a farkon 2022, ta sha alwashin tara kuɗaɗen haraji har Naira tiriliyan 10.44.
A ɓangaren fetur da makamantan sa ne gwamnatin tarayya ta ce ta tara Naira tiriliyan 4.2, kenan an wuce kintacen da aka yi a farkon shekara.
Wannan karo dai FIRS ta zarce adadin da ta yi kintacen za ta iya kaiwa.
“A shekarar 2021 an tara kuɗaɗen shiga naira 6.4. To dalilin yin amfani da tsarin TaxPro-Max wurin karɓar haraji.
Daga cikin kamfanonin da suka amfana da ɗaga ƙafar ta adadin Naira tiriliyan 1.56, NNPCL, Dangote Limited, Ɗangote Flour Mills, NPA, Nigeria LNG, BUA, MTN Nigeria, GZ Industries Limited, Transcorp Group, sai Access Bank da sauran su da dama.
Discussion about this post