Shugaba Bola Tinubu ya gana a keɓance da wasu shugabannin duniya guda uku, a wurin taron Ƙungiyar Ƙasashen Masu Ƙarfin Arziki na Duniya, wato G20, da ke gudana a New Delhi, babban birnin ƙasar Indiya.
Shugabannin ƙasashen uku da Tinubu ya gana da su ɗin dai sun haɗa da Joe Biden na Amurka, Shugaban Jamus da kuma Shugaban Koriya ta Kudu.
Najeriya ta halarci taron matsayin ‘yar kallo, wadda aka gayyata domin ganin yadda taron ke gudana.
Sannan kuma Najeriya ta kalli yadda aka yi wa kungiyar AU ta Afrika rajista a matsayin mamba ta ƙungiyar G20.
Fadar Shugaban Amurka ta White House ce ta yi sanarwar ganawar a cikin wata sanarwar da aka ce, “Shugaba Joe Biden ya gana da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a yau, a keɓance a New Delhi, Indiya domin ƙarfafa daɗaɗɗiyar dangantakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya.”
Haka kuma Tinubu ya sàke keɓancewa da Shugaban Jamus da na Koriya ta Kudu a wurin taron na G20, wanda aka kammala.
Biden ya jinjina wa sabon tsarin farfaɗo da tattalin arzikin da Tinubu ya bijiro da shi.
Kuma ya yaba da rawar da Tinubu ke kan takawa a shugabancin ECOWAS.
Kan haka ne ya ce G20 sun gayyaci Najeriya ta halarci taron a matsayin ‘yar kallo, domin ita ce mafi ƙasaitacciyar ƙasa mai dimokraɗiyya a Afirka, kuma ta gaba a ƙarfin tattalin arziki a Afrika ɗin.
Shi ma Ajuri Ngalale, Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Bola Tinubu, ya ce shugaban na Najeriya ya yi wata ganawar da Shugaban Jamus, Olaf Scholz, kuma sun tattauna batutuwan haɗa ƙarfin inganta tattalin arzikin ƙasa tsakanin Najeriya da Jamus.
Scholz ya bayyana wa Tinubu aniyar sa ta kawo ziyara Najeriya a cikin Oktoba.
Haka kuma Tinubu ya gana da Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol dangane da haɗa guiwar kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki.
Discussion about this post