Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa ɓarnar da ta’addancin Boko Haram su ka yi a Arewa maso Gabas ta kai Dala Biliyan 9.
Ya ce Jihar Barno kaɗai sun yi ɓarna za ta kai ta Dala 6.8.
Shettima ya kuma yi kira ga Hukumar Bunƙasa Arewa maso Gabas (NEDC) ta faɗaɗa ayyukan ta wajen gina titina, kada ta tsaya kawai iyar ayyukan da aka ce su kaɗai za ta yi.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi wannan bayanin a Maiduguri, lokacin bukin buɗe rabon kayan tallafi a Arewa maso Gabas, da kuma buɗe fara aikin titin zuwa Jere.
Taro kuma ya zo daidai da ranar taron Gwamnonin Arewa maso Gabas na 8.
“Ina so wannan hukuma ta faɗaɗa ayyukan ta zuwa aikin gina titina a faɗin jihohin Arewa maso Gabas, kamar Gombe zuwa Bauchi, Maiduguri-Damboa-Biu da Gujiba-Biu da sauran su.”
Ya ce idan aka gyara titinan, ‘yan Najeriya za su ci moriyar titinan, ba sai ‘yan yankin Arewa maso Gabas kaɗai ba.
“Ɓarnar da Boko Haram su ka yi wa Arewa maso Gabas ta kai Dala Biliyan 9. A Barno kaɗai za ta kai Dala Biliyan 6.8. To sun yi ɓarna kuma a Yobe, Adamawa, Gombe, Bauchi da Taraba.
“Idan da a ce Arewa maso Gabas ƙasa ce, to da talaucin mu ya zarce na Chadi, Afghanistan da Nijar.” Inji Shettima.
Shettima ya ƙaddamar da fara rabon kayan tallafi na Naira biliyan 15 a ƙananan hukumomi 110 na yankin Sanatoci 18 a faɗin Arewa maso Gabas.
Discussion about this post