Wani lauya mai suna Douglas Ogbankwa, ya bayyana yadda jami’an SSS suka ci mutuncin sa ta hanyar lakaɗa masa dukan tsiya, gaggaura masa mari, jan shi ƙasa da kuma kulle shi a Hedikwatar su ta Jihar Legas.
Ogbankwa ya je ofishin ne domin ya raka wani wanda ya ke karewa, bisa gayyatar da SSS suka yi masa, domin ya amsa tambayoyi a ofishin su ka wata matsala.
Ogbankwa wanda kuma shi ne Daraktan Tsare-tsare na Ƙungiyar Lauyoyi ta Afrika, ya bayyana iftila’in da ya ce ya same shi a cikin shafin sa na Tiwita.
Ya ce yanzu haka kwana ya ke ya na tashi a cikin tsaron ko a wane lokaci zai iya rasa ran sa. Kamar dai yadda ya bayyana a ranar Talata.
“A yanzu haka ina cike da tsoron halin da rayuwa ta ke ciki, idan na tuna yadda wani jami’in SSS ya nuna ni da bindiga ya ce, ‘idan ka ƙara zuwa nan Ofishin DSS, zan ɗirka maka bindiga.”
Haka ya bayyana a lokacin da ya ke bayanin irin yadda ta ƙarke tsakanin sa da su a ofishin na su.
DSS dai na nufin ‘Department of State Service’, kuma su suka ƙaƙaba wa kan su wannan suna, amma sunan da tsarin mulkin Najeriya ya raɗa masu shi ne ‘State Security Service’s, wato SSS.
Ogbonkwa ya ce an riƙa sharara masa mari sannan aka ja shi a ƙasa girrr, har zuwa magarƙamar da aka kulle shi a ƙarƙashin ƙasa.
Ya bayan sun isa wurin jira a ofishin SSS, sai aka turo wata mace jami’a ta ce wanda ya ke karewa ya biyo ta ya je ya rubuta bayani.
Shi kuma lauyan sai ya ce ai sai dai wanda ya ke karewa ɗin ya rubuta bayani a gaban sa shi ma ya na wurin, kamar yadda Dokar Laifuka ta Ƙasa ta 2015 ta tanadar.
“Ai haka da ce sai wani Babban Jami’in Ƙaddamarwa (PSO) ya ƙaddamar min. Ya fara kwartsa min ihu ya na cewa na koma, kada na bi su.
“Nan take na ce ya daina yi min tsawa, don ni ba ƙaramin yaro ba ne. Kuma ai Ofishin SSS na Gwamnantin Tarayya ne, ina da ‘yanci. Nan na ce wa wanda na ke ƙara mu fice kawai.
“Ai kawai sai jami’an su ka ce a kulle ƙofa, kada a bari mu fita, sun kama ni.”
Ya ce daga nan ogan su ya ce cakuɗa ni. Ai kuwa sai ji na yi sun rufe ni su na gaggaura min mari. Kafin na ankara an gaura min mari bakwai zafafa. Wasu ma daga mai dunƙula hannu ya yi min ƙulli, sai mai kai min naushi.
“Na miƙe da ƙyar na ce to wannan dai ba aikin SSS ne ku ke yi ba ƙadamusancin ku ne kawai ku ke yi.
“Suka ce min ai su yaran Shugaban Ƙasa ne, za su iya kashe ni, kuma ba abin da zai faru.”
Wannan bayani da ya rubuta ya janyo baƙaƙen kalamai da zafafan kalmomi kan jami’an SSS daga masu karatu.
Wata zaƙaƙurar da ta taka rawa a lokacin zanga-zangar #ENDSARS a cikin 2020, cewa ta yi, “Najeriya ƙasa ce wadda dokar ta a kan takarda kawai ta ke, ba a aikace ba.” Inji Rinu Oduala.
Discussion about this post