Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, wato SSS, ta ce ta gano wasu marasa kishin ƙasa na ƙulle-ƙullen tayar da tarozoma a ƙasar nan domin yin cin fuska ga Gwamnatin Tarayya da kuma jami’an tsaro, dangane matsalar raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fuskanta.
SSS sun bayyana haka a ranar Litinin a Abuja, ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar, Peter Afunanya.
Afunanya ya ƙara da cewa rahotonnin leƙen asiri sun tabbatar da cewa daga cikin marasa kishin da ke ƙulle-ƙullen shirya tarzomar, akwai ‘yan siyasa waɗanda ke haɗa kawunan shugabannin ƙungiyoyin ɗalibai, ƙungiyoyin ƙabilu daban-daban, matasa da sauran marasa kishin, domin su shiga zanga-zangar.
Ya kuma ce hukumar ta gano wani gungun ‘yan siyasa a cikin manyan masu ƙulle-ƙullen shirya tarzomar.
SSS ta ce ta zura masu idanu, tare da bibiyar dukkan kaidin da su ke ƙoƙarin kitsawa, domin ta hana su aiwatarwa.
Afunanya ya ce babban burin maso shirya zanga-zangar shi ne su ga ƙasar nan ta dagule, amma haƙar su ba za ta cimma ruwa ba.
“Dangane da hakan ne SSS ke shawarta da gargaɗin Shugabannin Jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare cewa su ka kunnen ɗaliban su kada su shiga cikin aikata aikin da-na-sani.
“Ya ce a shawarci ɗalibai da yin gargaɗi a gare su, da kuma jajircewar iyaye su tabbatar cewa ‘ya’yan su ba su afka hanyar tayar da fitintinu da tayar da hankalin jama’a.”
Wannan gargaɗi ya zo ne kwanaki biyu rak kafin ranar Laraba, ranar da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ce za ta yanke hukuncin shari’ar zaɓen shugaban ƙasa.
Haka kuma gargaɗin na SSS ya zo kwanaki biyu kafin ranar da NLC ta shirya gudanar da zanga-zangar game-gari.
Discussion about this post