Dangantaka ta yi mummunan ɓaci tsakanin Gwamna Obaseki na Jihar Edo da mataimakin sa, Philip Shaibu.
Munin dangantakar har ta kai ga an hana Shaibu shiga Gidan Gwamnatin Jihar Edo a Benin. An kulle ƙofa aka hana shi shiga harabar Gidan Gwamnati.
Cikin wata sanarwa da Shuaibu ya tura a shafin Tiwita, ya ce “Ga ni nan tsaye ƙerere bakin ƙofa, amma an kulle, an hana ni shiga.
Wani hadimin Gwamna Obaseki ya ce Mataimakin Gwamna ya na da damar ya tafi sabon ofishin sa ya zauna, amma ba zai shiga cikin tsohon ofishin sa da ke cikin Gidan Gwamnati ba.
An dai kulle ƙofar da Shaidu zai bi zuwa ofishin sa da ke cikin Gidan Gwamnati da kwaɗo da sarƙa tun kafin ya isa wurin da safiyar Litinin.
Dama an ɗauke ofishin Mataimakin Gwamna daga cikin Gidan Gwamnati, aka gina wani ba a cikin gidan ba. Hakan ta faru ne lokacin da alaƙa ta fara tsami tsakanin Gwamna Obaseki da mataimakin na sa Philip Shaibu.
Sai dai kuma shi Mataimakin Gwamna ya bayyana cewa har yau ba a sanar da shi cewa an maida ofishin sa waje daga Gidan Gwamnati ba, ballantana ya koma can ɗin.
“Har yau ba a rubuto min takarda cewa na kwashe kaya na daga ofishi na da ke cikin Gidan Gwamnati, na koma sabon ofis wanda ba a cikin Gidan Gwamnati ya ke ba. Ma’aikata na kaɗai aka sanar a hukumance, amma ni ba wanda ya sanar da ni.
“A Lokacin da na ke wannan maganar, ina tsaye na ƙerere bakin ƙofa, an kulle da sarƙa da garƙama-garƙaman kwaɗuna.” Inji Shaibu, yayin da yake magana da wani, wanda ba a san ko wane ne ba. Ta wayar tarho dai su ka yi maganar.
Wani hadimin Shaibu da ya nemi a ɓoye sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mataimakin gwamnan ya shafe awa ɗaya bakin ‘get’ a tsaye, ya na ƙoƙarin samun Gwamna Obaseki ta waya, amma bai yi nasara ba. Haka ya gaji ya koma gida.
Daga nan ya tambayi Kwamandan Dakarun Gidan Gwamnati mai suna Ibrahim Babatunde, wanda ya shaida masa cewa an ba shi umarni “daga sama” kada su bari Mataimakin Gwamna ya shiga. Wato ya na nufin umarni ne daga gwamna kenan.
Shi ma Babban Jami’in Tsaron Gidan Gwamnati, Williams Wabba ya Yi magana da Mataimakin Gwamna ta waya, har ya yi alƙawarin cewa ga shi nan tafe yanzu-yanzu, amma har Shaibu ya gaji da jira ya bar wurin bai je ba.
Hadimin Shaibu ya ce abin da kawai Mataimakin Gwamna ke buƙata shi ne sanarwar a rubuce kamar yadda doka ta tanadar cewa ya koma sabon ofishin sa. “To amma shi Gwamna ya nuna ba ya sake son ganin sa kusa da shi kwata-kwata.”
Discussion about this post