A wata tattaunawa da aka yi da Shugaba Bola Tinubu a lokacin kamfen, kafin zaɓen shugaban ƙasa, ya shaida wa BBC cewa shi da shugaban lokacin Muhammadu Buhari, kowa daban ya ke da kowa.
“Ba ɗaya na ke da shi ba. Mun sha bamban. Ni Bola Tinubu na ke, shi kuma Muhammadu Buhari.”
Tun daga ranar da aka rantsar da Tinubu, ya riƙa ƙoƙarin ganin ya tabbas ya na nuna cewa shi ba kamar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba ne, duk kuwa da cewa su biyu ɗin ‘yan jam’iyya ɗaya ne, wato APC.
A alaƙar su biyu ɗin da jam’iyyar su, Tinubu ya nuna cewa sun sha bamban. Yayin da babu ruwan Buhari da shiga ya sasanta duk irin rikice-rikicen da ke kunno kai a APC, shi kuwa Tinubu ba hakan ya ke ba.
Misali, rikicin jam’iyya ya tafi da kujerar shugabancin Adams Oshiomhole a cikin 2020. Sai Buhari ya damƙa jam’iyya a hannun gwamnoni, ta hanyar naɗa Shugabannin Riƙo a ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe.
A shekarar da ta gabata ma gwamnoni sun yi ƙarfa-ƙarfa, su ka takura Buhari ya amince ya ba Abdullahi Adamu shugabancin APC. Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da aka yi da shi.
Tsohon Mashawarci Kan Harkokin Shari’a na APC, Muiz Banire, cewa ya yi lokacin da Buhari ya yi ƙoƙarin ya nuna jarunta a harkokin APC, sai ya ɗauki matakin da ba daidai ba, wato gurguwar dabara.
Yanzu kuwa ɗaukar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi a matsayin Shugaban APC da kuma Ajibola Bashiru a Matsayin Sakataren APC, ya nuna cewa Tinubu ya sha bamban da Buhari. Ganduje da Bashiru duk magoya bayan Tinubu ne ga gidi.
Daukar APC a damƙa wa Ganduje da Bashiru ya nuna cewa ba sauran yadda Ƙungiyar Gwamnonin APC za su sake yin wata ƙarfa-ƙarfa a APC a ƙarƙashin su Ganduje kenan.
Bayan saukar Adamu daga shugabancin APC, an yi zaton za a zaɓi Tanko Almakura, ɗan Jihar Nasarawa, inda Abdullahi Adamu ya fito, kamar yadda Sashe na 31.5 na Dokar APC ya gindiya.
Amma sai Tinubu ya yi watsi da wasu jiga-jigan APC da suka nuna kuskuren naɗa Ganduje, irin su Salihu Lukman.
Naɗa Ganduje Shugabancin APC Ya Karya Dokar APC – Salihu Lukman:
“Babu wani Sashe na APC da ya bai wa wani ko da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ƙarfin ikon naɗa wa jam’iyya shugaba ba bisa ƙa’idar da doka ta tanadar ba.
“Saboda haka a bisa dokar jam’iyya, daga Jihar Nasarawa Shugaban APC ya kamata ya fito.” Inji Lukman.
Amma Shugaba Tinubu ya yi biris da shi, ya goyi bayan Ganduje daga Jihar Kano, ɗan yankin Arewa maso Yamma. Maimakon a ɗauki shugaba daga Nasarawa, yankin Arewa ta Tsakiya.
Sai dai kuma tsawon watanni uku da hawan mulkin Tinubu, ya riƙe jam”iyya yadda ya ke so a ƙarƙashin jagorancin Ganduje da Bashiru.
Sannan Tinubu ya samu sa’ida biyo bayan saukar Lukman daga cikin shugabannin APC. Saboda Lukman ya taka rawa sosai wajen ɗaukar Oshiomhole, Mai Mala da Adamu daga shugabancin APC.
Kafin naɗa Ganduje, Lukman ya riƙa kai gwauro ya na kai mari ya na kururuwar haramcin naɗa Ganduje shugabancin APC.
Shi dama Tinubu a duk inda ya ke jagora, to jam’iyya ma cikin aljihun sa ta ke.
A 2006 ya kafa ACN, kuma ya miƙa jagorancin ta ga tsohon abokin sa, Bisi Akande.
Lokacin da aka yi ‘maja’ da ACN da ANPP a cikin 2013, sai da Tinubu ya tabbatar Bisi Akande ne ya zama Shugaban APC a farkon kafa jam’iyyar cikin 2013.
Lokacin da aka naɗa Gwamna Mai Mala Buni riƙon APC a 2020, Tinubu ya yi shiru, saboda Gwamnonin APC ne suka riƙa cin karen su babu babbaka a cikin jam’iyyar.
Bayan saukar Buni, an naɗa Abdullahi Adamu. Naɗin Adamu bai yi wa Tinubu daɗi ba, domin kaɗan ya rage ya rasa takarar shugabancin ƙasa, kasancewa Adamu ya goyi bayan Sanata Ahmad Lawan a lokacin zaben fidda gwani da kafin zaɓe.
Ko Biyayyar Ganduje Ga Tinubu Za Ta Sa Ya Yi Ƙarko A Shugabancin APC?:
Ganduje ya tsaya tsayin-daka ya na goyon bayan Tinubu a lokacin zaɓen fidda-gwani. Lokacin zaɓen Tinubu ya samu ƙuri’u 517,342 a Kano.
An yi tunanin bayan zaɓen shugaban ƙasa Tinubu zai rungumi Rabi’u Kwankwaso, saboda ganawar da su ka riƙa yi. Har wata muryar Ganduje aka riƙa yaɗawa, inda ya ke ƙorafin Tinubu ya watsar da shi, ya rungumi Kwankwaso.
Amma naɗa Barau Jibrin matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya sa an daina yaɗa ji-ta-ji-tar kusancin Tinubu da Kwankwaso. Saboda Jibrin mutumin Ganduje ne. Sannan kuma canja sunan Maryam Shetty a cikin naɗin ministoci ya sa an ga Ganduje na da ta-cewa a wurin Tinubu.
Sai dai kuma riƙe shugabancin jam’iyya abu ne mai wahalar gaske, ba wai yin biyayya kaɗai ga shugaban ƙasa ake buƙata ga shugaban jam’iyya ba.
Kwanan baya Gwamna Yahaya Bello ya ja zugar masu zanga-zanga a Hedikwatar APC, a kan ɗaukar Duro Meseko matsayin Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na APC, bayan murabus ɗin da Muritala Ajaka ya yi.
Ajaka ya koma SDP, ya tsaya takarar gwamna na zaɓen gwamnan Kogi da za a yi ranar 11 Ga Nuwamba, 2023.
Rahotonni sun ce Gwamna Bello ya fi so a naɗa wani daban. A ƙarshe dai Bello da Ganduje sun rufe ƙofa, sun sasanta.
Akwai ƙalubalen zaɓen gwamnoni har uku a ga Ganduje nan ba da daɗewa ba a jihohin Kogi, Imo da Bayelsa.
Sannan akwai rikice-rikicen APC a Ondo, tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da Mataimakin sa Lucky Aiyedatiwa, wanda ake ƙoƙarin tsigewa. Kuma a cikin 2024 za a yi zaɓen gwamna a Ondo ɗin.
Akwai kuma zaɓen fidda-gwani a jihohin Osun, Ekiti da Edo a 2024, har ma da Anambra.
Banire ya ce akwai abubuwa biyu waɗanda za su iya zama babbar matsala da barazana ga Ganduje. Na farko rashin bin ƙa’idar da doka ta shimfiɗa. Na biyu kuma yin kaka-gida.
Idan kuma Kotun Ƙoli ta jaddada nasara kan Abba Yusuf a shari’ar zaɓen Kano, to naƙasu ne ga Ganduje. Idan kuna ta ce Nasiru Gawuna na APC ne halastaccen gwamna, to Ganduje zai ƙara samun ƙarfin guiwa kenan.
Discussion about this post