Wani shugaban APC na Mazaɓar Arigidi, Akoko ta Arewa maso Yamma cikin Jihar Ondo, mai suna Olumide Awolumate, ya jijjibgi Kwamishinar Harkokin Mata, Bunmi Osadahun.
Sai dai kuma wanda ya yi dukan ya ce ya yi hakan ne a ƙoƙarin sa na kare kan sa.
Amma kuma tuni APC ta dakatar da shi, sannan kuma jama’a da dama na ta kiraye-kirayen a kama shi sannan a hukunta shi.
Lamarin ya faru a ranar Asabar, inda aka riƙa watsa bidiyon da ya yi ta narkar ta da duka a soshiyal midiya.
Kakakin APC na Jihar Ondo, Alex Kalejaiye, ya bayyana cewa dakatar da wanda ya yi dukan daidai ne.
“Muna kuma sanar da shugabannin APC na Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma cewa an dakatar da Awolumate Olumide daga mamba na APC na Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma, har sai yadda hali ya yi.”
Shugaban APC na Jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya ce za a kafa kwamitin ladaftarwa kan Awolumate, domin a ladaftar da shi.
Ya ce yin hakan zai zama babban darasi ga saura.
Awolumate ya ce tun farko kwamishinar ce da kan ta ta ja zugar wasu ‘yan iagaliya su biyu, har da ɗan ta, wanda ɗan sanda ne, suka yi masa taron dangi a gidan sa.
“Ɗan ta wanda ɗan sanda ne, shi ya fara kai min naushi daga baya. Ni kuma na ga ba zan tsaya haka kawai a riƙa naushi na ba a gaban mata ta da ‘ya’ya na da abokai na.
“Yayin da rufar wa ɗan na ta da duka ni ma, sai kwamishinar ta shiga faɗan, suka riƙa duka na har da kujera. Kuma ta kekketa min riga.
“Ni ma da na ga haka, na ɗauki kujera na kwantsama mata.
“Daga nan sai na fara ganin bidiyo na yawo ana nuna na doke ta. Amma duk wanda ya kalli bidiyon ya san an yi masa siddabaru, an yanke wasu wurare. Gaskiya ban taɓa tsammanin hakan za ta faru ba. Domin har gina su ka same ni.” Inji shi.
Gwamnatin jiha da Rundunar ‘Yan Sanda duk su na kan bincike.
Discussion about this post