Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sunayen mutum biyu majalisar Dattawa domin naɗa su ministoci a gwamnatin sa.
Waɗanda aka aika da sunayen su sun haɗa da
Jamila Bio Ibrahim a matsayin ministan matasa, sai kuma Ayodele Olawande a matsayin ƙaramin ministan Matasa.
Tinubu ya umarci ministocin su yi aiki tukuru tare da haɗa kan matasan Najeriya domin cigaban su da kasa baki ɗaya.
Jihar Kaduna ce jiha ɗaya tilo da har yanzu ba ta da wanda ke wakiltar ta a majalisar zartarwa ta kasa, wato, har yanzu ba a naɗa minista daga jihar.
Duka sauran jihohin kasar nan na da wakili a majalisar.
An so a naɗa tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai minista, sai dai bayan tantance shi da majalisa suka yi, sun gano ya na da ƙorafe korafe da ya shafe tsaro, da mutane da bangarori suka kawo kan sa.
Hakan yasa aka dakatar da naɗashi inda daga baya ya janye daga zama ministan.
Tun bayan haka ba a aika da sunan wani ba minista daga jihar Kaduna din.
Discussion about this post