Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa wadda aka yanke hukunci ranar Laraba a Kotun Ɗaukaka Ƙara dai ta wuce, amma ta bar labarin da za a daɗe ana barkwanci a kan sa.
A zaman kotun, manyan shugabanni da su ka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Gwamnoni, manyan ‘yan siyasa, lauyoyi da ‘yan jarida sun cika kotun tun ƙarfe 9 na safiya.
An shafe sa’o’i kusan 13 ana yanke hukunci, amma duk bayan tsawon lokaci, ana tafiya hutu, sannan a koma kotu.
Zama ya yi zama, har sai da ta kai da yawa daga cikin masu zaman kallo da sauraren shari’a sun riƙa sharar barci a zaune.
Yayin da wasu ke angaje, wasu gyangyaɗi, wasu kuma likimo ko kashamo su ka yi. Ana ta zuba bayanan hukunce-hukuncen shari’a, su kuma sunan sharar barci.
Gwamnoni sun yi barci, sun yi angaje, kuma sun gyangyaɗa. Musamman wasu lauyoyi da dama sanye da alkyabbar lauya da hular lauyoyi sun sharari barcin su a zaune.
Su ma ‘yan jarida masu ɗauko labarai saboda daɗewar da aka yi ana bayanin hukunce-hukuncen shari’a, an nuno wasun su na barci a kotu.
Cikin waɗanda aka nuno kuwa har da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Bala Mohammed, Gwamnan Bauchi da wasu da dama.
Sannan kuma wakilan gidan talabijin na Channels TV News su ma an nuno su su na barci.
A soshiyal midiya an riƙa yin barkwanci ana cewa wasu ma har sai da miyau ya riƙa dalalowa daga cikin bakin su. Amma dai PREMIUM TIMES ba ta tabbatar da wannan ruwayar ba.
Discussion about this post