Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi kira ga masu jayayya da shi a kotu cewa tunda an sake jaddada nasara a kan sa, to su haƙura, a rungumi kishin ƙasa tare da su da magoya bayan su baki ɗaya.
Cikin sanarwar Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar bayan yanke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi fatali da ƙarar da abokan hamayya su ka shigar, Tinubu ya ce ya ƙara samun ƙwarin guiwar yin aiki ga ƙasa tuƙuru ba tare da nuna bambanci, ɓangaranci, ƙabilanci, addinanci ko nuna fifiko ba.
Ya ce babban muradin sa shi ne ciyar da Najeriya gaba da kuma kare dimokraɗiyya.
‘Ba Mu Yarda Da Hukuncin Kotun Tsammani Ba’ – Atiku, Obi, LP:
A na su ɓangaren, Atiku, Peter Obi da LP la’anci hukuncin kotu, za su garzaya Kotun Ƙoli.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Abubakar na PDP, takwaran sa na LP, Peter Obi da jam’iyyar LP ɗin, duk sun yi tir, tare da nuna rashin amincewa da sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wadda a ranar Talata ta jaddada nasarar da Bola Tinubu na APC ya yi.
Kotun mai alƙalai biyar a ƙarƙashin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta yi fatali da ƙararrakin da Atiku, Obi, LP da APM su ka shigar, bisa dalilin cewa sun kasa gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da za ta tabbatar da maguɗin da su ke zargin an tafka.
Sun bayyana cewa za su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin a bi masu haƙƙin rashin adalcin da su ka ce Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen na Shugaban Ƙasa ta yi masu.
Bayan kammala shari’ar wadda ta ɗauki sa’o’i 13 ana yanke hukunci, Sakataren Yaɗa Labaran LP, Obiora Ifor ya ce ba a yi adalci ba, “saboda ba a yanke hukunci daidai da abin da akasarin abin da ya faru a lokacin zaɓe ba. Kuma ba haka jama’a su ka so su ji daga kotun ba.”
Ya LP ba za ta gajiya ba har dai ta ƙwato wa mutane haƙƙin su na abin da su ka zaɓa, ta hanyar tabbatar da adalci a Kotun Ƙoli.
“Najeriya da duniya sun tabbatar da an yi fashin ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa na Fabrairu, 2023, amma kotu ta kauda kai, ta ƙi yin adalci. To ba za mu haƙura ba, sai mun dangana da Kotun Ƙoli.”
Discussion about this post