Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta aza ranar Laraba, 6 Ga Satumba za ta yanke hukunci, domin bayyana sakamakon shari’ar ƙararrakin da Atiku Abubakar da Peter Obi su ka maka Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, INEC da kuma Jam’iyyar APC.
Atiku wanda ya tsaya takara a zaɓen 2023 a ƙarƙashin PDP, da Peter Obi na LP sun garzaya kotun ne su na ƙalubalanta tare da ƙin amincewa da sakamakon zaɓen.
Jam’iyya ta uku cikin masu ƙarar iya ce APM ta uku a cikin masu ƙalubalantar nasarar da Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa.
Kusan wata ɗaya kenan bayan kammala sauraren ba’asin kowane ɓangare, kotu ta ce ta sallami kowa, amma za ta aza ranar da za a koma kotu, domin ta yanke hukunci.
A tsarin dokar Najeriya dai tilas wanda ke jayayya a shigar da ƙara, a yi saurare zuwa yanke hukunci a cikin kwanaki 180. Saura makonni biyu dai wa’adin ya cika.
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ce wadda a can ne ake yin shari’ar ta fitar da sanarwar cewa za ta yanke hukuncin a ranar Laraba mai zuwa, kamar yadda aka fitar da sanarwar a ranar Litinin.
Babban Rajistara na Kotun Ɗaukaka Ƙara, Umar Bangari, ya ce za a nuna shari’ar yanke hukuncin kai-tsaye a gidajen talbijin.
Ya ce za a nuna yanke hukuncin a gidajen talbijin kamar yadda mutane su ka buƙaci a yi, amma a baya kotun ta ƙi amincewa a nuna kai-tsaye a baya.
Atiku da Peter Obi kowanen su ya shigar da ƙara cewa shi ya yi nasara ba Tinubu ba. Iƙirarin kowanen su shi ne ko dai a ba shi nasara kawai, ko kuma a sake zaɓe sabo, wanda kuma su ka nemi kada kotu ta bari Tinubu ya sake shiga zaɓen.
Akwai dai ƙararraki har biyar da aka shigar kan rashin amincewa da nasarar Tinubu. Amma an janye guda biyu tun kafin a fara sauraren ba’asin shari’ar.
Alƙalai biyar ne za su yanke hukuncin, cikin su har da shugaban su, Haruna Tsammani.
Discussion about this post