Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, ta yi fatali da ƙarar da jam’iyyar APM ta maka Bola Tinubu, inda ta ce bai halasta a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ba.
Yayin da ya ke karanto jawabin korar ƙarar, Shugaban Gungun Alƙalai 5, Haruna Tsammani, ya koro dalilan korar ƙarar, bisa doron hujjar cewa batun cancanta ko rashin cancantar ɗan takara kamar muƙamin mataimakin shugaban ƙasa, matsala ce ta ‘yan cikin jam’iyya, ba matsalar ɗan wata jam’iyya ba ce.
Haka nan kuma ya kawo hujjar cancantar Kashim Shettima zama mataimakin takarar Tinubu, sannan kuma an yi fatali da ƙorafin rattaba sunan Ibrahim Masari a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, kafin a maye gurbin sa da Kashim Shettima.
Wannan jarida ta ruwaito cewa Atiku, Obi da Tinubu ba su halarci zaman sauraren yanke hukunci ba
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi duk ba su halarci zaman sauraren yanke hukunci a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wanda ke gudana a yau.
Yayin da Tinubu ya fice daga ƙasar a ƙarshen mako domin halartar taro a Indiya, ba a san dalilin rashin halartar Atiku da Obi ba.
An samu dafifin manyan ƙasa da manyan ‘yan siyasa a sauraren yanke hukunci a kotu.
A yau Laraba, ranar da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke cewa za ta yanke hukunci kan ƙararrakin da Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP da Peter Obi na LP su ka kai.
Tun da safe manyan shugabannin ƙasa da manyan ‘yan siyasa su ka yi dafifi cikin kotu, domin zaman sauraren yanke hukunci.
Daga cikin su akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro na Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu da kuma Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Daga baya gwamnoni da dama sun isa, ciki har da Hope Uzodinma na Imo da wasu da yawa.
Alƙalai biyar ne za su yanke hukuncin, a ƙarƙashin jagoran su Mai Shari’a Haruna Tsammani.
Daga cikin alƙalan akwai maza huɗu da kuma mace ɗaya.
Dukkan su Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara ne. Duk wani hukuncin da su ka yanke za a iya ƙalubalantar sa a Kotun Ƙoli.
Atiku da Obi na so ko dai a soke zaɓe, tare da hana Tinubu sake tsayawa takara, ko kuma kotu ta bai wa kowane daga cikin su biyun.
Discussion about this post