A ci gaba da warware zare da abawar shari’ar zaɓen shugaban ƙasa tsakanin Peter Obi da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta kori ƙarar Peter Obi, inda ya yi zafin yin aringizon ƙuri’u ga Tinubu na APC.
Mai Shari’a Haruna Tsammani ya ce Peter Obi ya gabatar wa kotu da kwafen takardun sakamakon zaɓe har 18,000 masu dishi-dishi, amma ya kasa gabatar da rumfunan zaɓe da akwatinan da ya kwafo kwafen takardun har 18,000.
Kotu ta ce ta karɓi ƙoƙarin aringizo da Peter Obi ya shigar, amma kuma ya kasa gabatar da wurare, runduna da shaidar akwatinan zaɓen da ya ce an yi aringizo ɗin.
Kafin nan kuma sai da kotu ta yi fatali da shaidar ƙwararriyar injiniyar manhaja ta Peter Obi, ta ce ‘yar jam’iyyar LP ce, har takara ta taɓa tsayawa.
Jagoran Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, ya ce kotu ba za ta karɓi shaidar ƙwararriyar masaniyar logar yanar gizo da manhaja, wadda ɗan takarar shugaban ƙasa na LP Peter Obi ya gabatar a baya ba.
Ya bayyana cewa lauyoyin Tinubu ne su ka bayar da hujjar cewa masanin kuma injiniyar mai suna Mpeh Ogar ba ‘yar-ba-ruwan-mu ba ce, ‘yar jam’iyyar LP, wanda kotu ta ce ta tabbatar har ma takara ta taɓa tsayawa a ƙarƙashin LP.
Tsammani ya ce kotu ba za ta amshi shaidar ta ba, saboda ɗan ɓangaranci ne. A irin wannan shaida kuwa a cewar kotu, ana ɗauko ƙwararren da ba shi a wata alaƙa, nasaba ko kusanci da jam’iyya ne ko ɗan takarar da ya shigar da ƙara.
Discussion about this post