Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Abubakar na PDP, takwaran sa na LP, Peter Obi da jam’iyyar LP ɗin, duk sun yi tir, tare da nuna rashin amincewa da sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wadda a ranar Talata ta jaddada nasarar da Bola Tinubu na APC ya yi.
Kotun mai alƙalai biyar a ƙarƙashin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta yi fatali da ƙararrakin da Atiku, Obi, LP da APM su ka shigar, bisa dalilin cewa sun kasa gabatar wa kotun gamsassun hujjojin da za ta tabbatar da maguɗin da su ke zargin an tafka.
Sun bayyana cewa za su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin a bi masu haƙƙin rashin adalcin da su ka ce Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen na Shugaban Ƙasa ta yi masu.
Bayan kammala shari’ar wadda ta ɗauki sa’o’i 13 ana yanke hukunci, Sakataren Yaɗa Labaran LP, Obiora Ifor ya ce ba a yi adalci ba, “saboda ba a yanke hukunci daidai da abin da akasarin abin da ya faru a lokacin zaɓe ba. Kuma ba haka jama’a su ka so su ji daga kotun ba.”
Ya LP ba za ta gajiya ba har dai ta ƙwato wa mutane haƙƙin su na abin da su ka zaɓa, ta hanyar tabbatar da adalci a Kotun Ƙoli.
“Najeriya da duniya sun tabbatar da an yi fashin ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa na Fabrairu, 2023, amma kotu ta kauda kai, ta ƙi yin adalci. To ba za mu haƙura ba, sai mun dangana da Kotun Ƙoli.”
‘Za Mu Ɗaukaka Ƙara’ – Atiku da Peter Obi:
Da ya ke wa manema labarai bayani bayan yanke hukunci, lauyan Atiku Chris Uche, ya ce tuni har ya samu umarni daga Atiku Abubakar cewa ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.
Shi ma Livy Uzoukwu, lauyan Peter Obi, ya ce za su garzaya Kotun Ƙoli.
Da aka tambaye shi cewa kotu ta ce sun kasa gabatar da ƙwararan hujjoji, sai ya yi gargaɗin cewa idan aka yi wasa a ƙasar nan, to darajar hujja a kotu za ta dishe baki ɗaya.
“Ya kamata mu yi taka-tsantsan a ƙasar nan. Idan ba haka kuwa, duk ranar da waɗanda aka yi wa maguɗi a zaɓe, sannan kotu ta ƙi karɓo masu haƙƙin su saboda sun kasa kawo hujjoji, to za su da ɗauki matakin da zai yi wa ƙasar nan kyau ba.”
Discussion about this post