Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana cewa shi da NNPP za su ɗaukaka ƙarar hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a Kano, inda ta soke nasarar da ya samu.
A wata gajerar tattaunawa da BBC Hausa, Yusuf ya bayyana hukuncin kotun a Kano da cewa zalunci ne ƙarara.
Ya ce a wannan gwagwarmaya da su ke yi ta kishi ce na Jihar Kano, ba don kan su su ke yi ba.
Ya ce nan da kwanaki biyu, lauyoyin su za su harhaɗa bayanan da za su haɗa su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Yayin yanke hukuncin, Kotu ta ce Abba ya yi wa Gawuna rata da kuri’u 128,900, to amma yanzu Kotu ta zaftare wa Abba Kuri’u 165,633, Gawuna na APC ya yi nasara kenan da kuri’u 36,733.
Discussion about this post