Shugaba Bola Tinubu ya ƙara matsa lambar ganin cewa ya yi duk ƙoƙarin da zai yi, don ya ga Kotun Amurka ba ta bada umarni ga Jami’ar Chicago ta bayar da kwafen satifiket ɗin karatun sa ga Atiku Abubakar ba.
Bayan Tinubu ya karɓi hukuncin da Kotun Gundumar Arewacin Illinois ta yanke, cewa ta dakatar da umarnin a damƙa kwafen takardun shaidar Tinubu ga Atiku, sai kuma Tinubu ya sake shigar da wani ba’asi, inda ya roƙi kotu cewa ba ya so a damƙa kwafen satifiket ɗin ga Atiku kwata-kwata.
Lauyan Tinubu da ke zaune Amurka, mai suna Oluwole Afolabi ne ya shigar da riƙon a madadin Tinubu, bisa dalilai biyu da ya gabatar wa kotun.
Na farko dai ya ce ko an damƙa wa Atiku Abubakar satifiket ɗin TInubu da sauran kwafe-kwafen takardun makarantar sa, ba za su amfana masa da komai ba a kotun Najeriya.
Dalili na biyu kuma cewa ya yi, idan aka damƙa wa Atiku kwafe-kwafen takardun makarantar Tinubu, to an ba shi lasisi ne na shiga gonar da ba tasa ba, domin laluben sirrin wani wanda shi ma doka ta hana a bai wa wani ƙofar shiga ya binciki sirrin rayuwar sa.”
Ya roƙi kotu ta yi watsi da buƙatar Atiku kawai.
“Ko ma an damƙa takardun, babu abin da za su tainana masa, sai kawai don ya na ɗan adawa ne, zai yi bincike kan wani sirrin abokin adawar sa.”
Atiku ya ce “za a yi min illa idan aka sakar wa Atiku takardun shaidar karatu na a Jami’ar Chicago.”
Ya ce a baya ai Atiku ya samu kwafen, amma ta bayan fage, kuma ya riƙa ragargaza sa a kan su.
Ya ƙara cewa ba gaskiya ba ce da Atiku ya ce Kotun Ƙoli a Najeriya za ta iya amfani da kwafen takardun wajen yanke hukunci a ƙarar zaɓen 2022 da Atiku ya shigar.
Discussion about this post