• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    court

    Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    ‘Yan sanda sun kama wani da ya shahara wajen yi wa mutane damfara ta Facebook

    #EndSARS: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan zargin kisan masu zanga-zanga a Lekki, Lagos

    Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

    Abuja bill-board

    RASHIN TSARO – Abuja ta zama matattarar batagari da masu sace mutane – Dan majalisa

    NYSC

    Za a yi wa shirin yi wa kasa hidima, NYSC, garambawul – Gwamnati

    Gwamnatin Tinubu ba za ta ƙaƙaba wa jama’a takunkumin hana magana ba – Minista

    SHIRIN WAYAR DA KAI: Ministan Yaɗa Labarai ya kafa kwamitin tsara daftarin cusa ɗa’a, kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u

    KISAN MASU MAULIDI: Mun samu gawarwaki 85 – Hukumar Agajin Gaggawa

    KISAN MASU MAULIDI 85: Sarkin Musulmi, Shehunan Tijjaniya, Dattawan Arewa da Shugaban Izala sun ce ba za a yafe ba

    TARON COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Najeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba – Minista Idris

    Uba Sani ya yi alhini da ta’aziyyar kisan dandazon ƴan maulidi a Kaduna, ya umarci a gudanar da bincike

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Saura ƙiris Liverpool ta zubda abin faɗi a wasan Premier League na ranar Lahadi

    MESSIN DAI: Leo Messi ya lashe kyautar ɗan kwallon duniya ta Ballon d’Or a karo na takwas

    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Dalilin da ya sa na ziyarci Tinubu – Uba Sani

    BIDIYO: Tinubu masoyin ‘Yan jarida ne – Idris

    Timipre-Sylva

    TANGARƊA A APC: Kotu ta hana Sylva, tsohon Ministan Fetur tsayawa takarar zaɓen gwamnan Bayelsa

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

No Result
View All Result

SAKAMAKON AMBALIYA: Yadda yunwa ke nuƙurƙusa da kisan talakawa a yankunan Arewa

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 23, 2023
in Manyan Labarai
0
Flood in Jigawa

Flood in Jigawa

Babban jidali da bala’i a wayi gari magidanci mai iyali ya shafe kwana da kwanaki bai ci ba, kuma bai samu ya kai wa iyalin sa sun dafa sun ci, kai ko da ɗanyen ne ma sun ci.

Bala’in da ya zarce wannan muni shi ne idan matsalar babu ɗin ta kai gargarar da har yunwa ɗin ta kai ga yi wa marasa galihu ɗauki-ɗai-ɗai, daga duniya ta na cilla su lahira.

Haka ta faru da wata budurwa mai suna Aisha, wadda babu wanda ya san musabbabin rasuwar ta, har sai bayan an binne a kabari, kafin a tashi sai mahaifin ta ya sanar da masu makoki cewa, “babu abin da ya samu A’isha, tsananin yunwa ce ta kashe ta!” Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.

Mahaifin A’isha mai suna Malam Garba (mun ɓoye sunan sa na ainihi), ya fito ne daga wani yanki a Jihar Adanawa. Ya shaida cewa yunwa ce ta kashe ‘yar sa ta farko, Aisha. Ya ƙara da cewa raɗaɗin tsadar rayuwa ya afka masa shi da iyalin sa sakamakon daminar bana ba ta yi masa albarka ba.

Ya ce, “iyali masu fuskanci tsananin yunwar da mukan shafe makonni da dama ba a iya ɗora girkin abinci sau biyu ba.

“Da A’isha ta ga matsalar rashin abincin sai ƙaruwa ta ke yi, sai ta ce ‘ai da yunwar banza gara mai dalili’, sai ta fara azumin nafila a kullum, don kawai ƙannen ta su samu su ɗan riƙa haɗawa da na ta kason abincin su na ci.

“Marigayiya A’isha ta sadaukar da abincin ta ga ƙannen ta, don su samu su ɗan riƙa ci kafin mu kwanta barci.

“Wasu lokuta kuma idan A’isha ta samu ta ɗan ci wani abu a lokacin buɗa-baki, ta na sahur da asubahin ma gagarar ta ya ke yi.

“Ranar da ta ɗauki azumi na 30, sai ta fara kyara aman jini a duk lokacin da ta yi tari. Bayan kwanaki sai rai ya yi halin sa.” Inji Malam Garba, mahaifin ta.

Jama’a sun tausaya wa mahaifin A’isha bayan sun ji wannan labari marar daɗin ji, kuma mai dugunzuma zukata. Wasu kuma sun riƙa yin alƙawarin tallafa wa iyalin Malam Garba, tare da taimaka wa ƙannen Aisha domin su tsira daga yunwar da ta nuƙurƙusar da dukkan ‘yan gidan su.

A shekarar 2022 dai an fuskanci gagarimar ambaliya a yankuna da yawa na Arewacin Najeriya, sakamakon ruwan sama mai yawa, kuma mai ƙarfi.

Koguna da ƙoramu da gulabe sun cika maƙil. Madatsun ruwa sun cika, sun batse har sun riƙa ɓallewa, musamman madatsun ruwan Kamaru da suka haddasa ambaliya a jihohi 31 daga 36 na Najeriya.

Cibiyar Bincike ta Majalisar Ɗinkin Duniya, mai suna UNOSAT, ta bayyana cewa tsakanin 13-17 ga Oktoba, 2022 ambaliya ta yi wa sama da mutum miliyan 6.6 babbar barazana. Kuma kusan fiye da murabba’in kilomita 30,000 ne ambaliya ta mamaye.

Jihar Adamawa na cikin jihohin da ambaliyar ta fi yi wa babbar ɓarna, inda aka ƙiyasta ta shafi sama da mutum 260,000 a jihar. Kuma kuma ambaliya ta mamaye kilomita 1,000 a jihar, tare da lalata dukkan amfanin gonar da ke wuraren da ambaliyar ta mamaye.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jiha, ta ce ambaliyar ta afku sanadiyyar ruwa mai ƙarfin da aka riƙa yi daga 11 zuwa ga Yuli, har zuwa 24 ga Oktoba, 2022.

Ambaliyar ruwan da ya riƙa darkakowa daga Kamaru ya haddasa cika da batsewar Kogin Benuwai, wanda hakan ya haddasa ambaliya a Jihar Adanawa.

Sannan kuma ambaliyar ta ƙara muni bayan Kamaru ta ɓallo ruwan Madatsar Ruwa ta Lagdo, inda ruwan ya malalo Arewacin Najeriya, ya lalata amfanin gona da dukiya mai tarin yawa.

Shugaban SEMA na Jihar Adamawa, Suleiman Muhammad, ya ce “Binciken HNO na 2022 ya tabbatar da cewa sama da mutum miliyan 2.45 ne suka rasa muhallin su a Jihar Adamawa, su ka koma tsuguno a sansanonin masu gudun hijira.”

Wakilin mu ya je garin Gerio, ɗaya daga cikin garuruwan da ambaliyar ta fi yi wa mummunar illa.

Wani ɗan jarida mai suna Yakubu Abdullahi, ya shaida wa wakilin mu cewa tsawon sama da shekaru 30 kenan, duk lokacin da Kamaru ta ɓalle ruwan Dam ɗin Lagdo, sai ambaliya ta yi mummunar ɓarna a yankunan Najeriya.

Sai dai wani kuka ya ce ba fa laifin ruwan da Kamaru ke ɓallowa a kowace damina ne kaɗai ke haddasa masu asarar amfanin gona ba. Ya ce su kan yi noman rani da noman damina. Amma a shekarar 2021 sun fuskanci fari da ƙarancin ruwa daga dam ɗin Gerio. Ya ce kashi 80 zuwa kashi 90 bisa 100 na shinkafar da suka noma cikin 2021 duk bushewa ta yi, ba su ci gajiyar ta ba. Saboda Kamaru ba ta sako ruwa a shekarar ba.

“To da muka zuba shinkafa a 2022 mai yawan gaske domin noma har da wadda muka yi asara a 2021, sai ruwa mai ƙarfi ya zame mana bala’i, duk ya yi tafiyar-ruwa da shinkafar a cikin gonakin mu.”

Ya nuna cewa ruwan da ke malalowa daga Kamaru ba bala’i ba ne a wurin su. “Ba za mu yi saurin cewa mun yi nasara ba kam. Amma abin da ke addabar mu shi ne ruwan sama mai ƙarfin gaske, ba ruwan da ke malalowa daga Kamaru ba.”

Tags: AmbaliyaLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

‘Kwankwaso ne ya kada mu a shari’ar Kano saboda kwaɗayin kujerar minista a gwamnatin APC – Abbas Akande

Next Post

SHUGABANCIN APC: Ko biyayyar da Ganduje ke wa Tinubu za ta sa ya yi kargo a ɗigirgiren shugabancin APC?

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Ganduje ya naɗa Shugaban Riƙon Hukumar Hana Cin Hanci ta Kano, bayan dakatar da Muhyi Magaji

SHUGABANCIN APC: Ko biyayyar da Ganduje ke wa Tinubu za ta sa ya yi kargo a ɗigirgiren shugabancin APC?

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda farashin magungunan Mura, Zazzabi, da sauransu suka yi tashin gwauron zabi cikin shekaru Hudu a Najeriya
  • DUBU TA CIKA: ‘Yan sandan Adamawa sun cafke wani matashi da ya rika yi wa babbar Zakara fyade yana lalata da wannan Zakara
  • Gwamnati ta fara horas da ma’aikatan lafiya hanyoyin dakile yaduwar cutar diphtheria
  • Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu
  • KISAN TUDUN BIRI: Uba Sani ya zama Uba da Uwa ga ya’yan da suka rasa iyaye a sanadiyyar harin

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.