Wani ma’aikacin gwamnati Surajudeen Olasinde ya bayyana yadda ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da matarsa Mistura, ‘ya’yan sa mata biyu Fatima da Hauwa a Abuja.
Olasinde ma’aikacin hukumar NNRA ya ce an yi garkuwar da iyalansa ranar 8 ga Satumba yayin da suke hanyar komawa gida a cikin mota kirar ‘Toyota Highlander’ dake rukunin gidajen ‘Starwood’ A Abuja.
“ Maharan sun tafi da iyalaina ciki daji da misalin karfe bakwai na yamma bayan sun kama su a hanyar zuwa gida dake unguwar ‘Kabusa Garden’.
“ Mun kira ‘yan sandan dake Galadimawa da jami’an tsaro na SSS inda suka fara farautar maharan a cikin daren da aka yi garkuwa da su.
“ A lokacin da abin ya faru bana Abuja ina jihar Kwara wurin aiki amma bayan na dawo na samu labarin cewa maharan sun kira dan uwan mata na suna bukatar kudin fansa har naira miliyan 100 inda daga baya suka rage zuwa miliyan 50, zuwa miliyan 10 sannan zuwa iya kudaden da muke da shi.
“Mun iya hada naira miliyan 2,840,000 Kuma maharan sun fada mana cewa mu kai kudin kauyen Kubusa.
“Bayan da suka karbi kudaden ne iyalina suka dawo gida da misalin karfe 8 na yammacin Asabar.
Ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ministan Abuja Nyesome Wike da su yi gaggawar samar da tsaro domin kare rayukan mazauna Abuja.
Shima Shugaban mazauna rukunin gidajen ‘Starwood’ Kayode Adedoyin ya yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen garkuwa da mutanen da ake yawan yi a yankin su.
Discussion about this post