Fitaccen ɗan wasan kwaikwayo na Hausa, a farfajiyar Kannywood, Mustapha Naburaska ya maida wa shugaban tace finafinai na jihar Kano, Abba Almustapha martani kan umarnin da ya bada na kowani ɗan fim ya je ya sabonta rajista da hukumar.
Idan ba a manta ba sabon shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano Abba Almustapha ya umarci duka ƴan fim da masu aiki a karkashin farfajiyar Kannywood su garzaya hukumar su sake sabonta rajistar su kan su ko kamfanonin su.
Rajistar ya shafi ƴan wasa, furodusoshi, masu hada fim, mawaka, da dai sauran su.
Sai dai kuma wannan umarni ya gamu da suka daga ƴan wasa da dama daga cikin ƴan wasan kannywood din.
A ranar Talata, fitaccen ɗan wasa Mustapha Naburaska ya soki wannan umarni cewa babu tausayi a cikin sa.
” Wannan abu sam babu tausayi a cikin sa. Da wanne ƴan kannywood za su ji da, abinci ko rashin aikin yi, ko ko sabonta rajistar da ba shi da amfani.
” Yanzu fa Kannywood kamar ‘kufayi’ ta zama, babu abinda ake yi cikin ta, kusan kashi 95 cikin 100 na masu hadahada a farfajiyar duk sun koma wasu sana’o’in ko zaman kashe wando don babu aikin.
” Tsakani da Allah, ko naira ₦5000 ce aka ce mutum ya biya ai akwai takura. Idan ya biya sai me, wurin da babu aikin yi yanzu a ciki.
” Yanzu fim a YouTub ake saka shi, kuma sai kana da tarin mabiya shine za ka rika samun kuɗi suna biyan ka. Wannan shine magana su waye suke iya haka.
Naburaska ya kara da cewa a ganin sa Almustapha ya yi gaggawar fadin sabonta lasisi. ” Abinda ya fi dacewa shine su maida hankali wajen lallaɓae gwamnati ta saka hannu a harkar, idan ta farfaɗo sai a yi maganan sabonta lasisi amma ba yanzu da babu komai ba sai kuma a tilasta mutane su sabonta lasisi. Lasisin me za su sabonta?.
Discussion about this post