Dakarun sojin Najeriya sun kashe Boko Haram/ISWAP 39 sun kama wasu guda 159 sannan sun ceto mutum 109 da aka yi garkuwa da su a cikin makonnin biyu da suka gabata.
Darektan yada labarai Edward Buba ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe Boko Haram/ISWAP 11 sun kama wasu 45 sannan sun ceto 34 da aka yi garkuwa da su kuma sun kama makamai da dama a kananan hukumomi Gwoza da Tarmuwa dake jihohin Borno da Yobe.
Ya ce dakarun sun kama manyan bindigogi kirar AK-47 6, bindiga kiran HK21 daya, bindiga kiran GPMG guda daya, bindiga kirar gida daya, da harsasai masu yawan gaske.
Sannan kuma da babura biyar, wayoyin hannu 8 da kudi naira 368,950.
Buba ya ce dakarun sojin sama sun kai wa mahara hari a maboyar su dake Wulde a jihar Borno.
A yankin Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kashe ‘yan bindiga biyu, sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su sannan sun kama wasu mahara 15.
Dakarun sun kama mahara biyu a karamar hukumar Jema’a a jihar Kaduna inda daya daga cikin maharan na daga cikin maharan da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.
Dakarun sun kama manyan bindigogi kirar AK-47 3, da wasu bindigogin sannan kuma da tarin harsasai ma su yawa.
Buba ya ce a nan ma an kama bindigogi da harsasai.
Ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ dake Area maso Yamma sun kashe mahara 12, sun kama wasu guda 33, sun ceto mutum 40, sun kama manyan bindigogi kirar AK-47 guda 3, babura 18 da wayoyi 3.
Haka kuma sojojin sama sun kashe ƴan bindiga a harin da suka kai musu a maɓoyar su.
Discussion about this post