Hukumar tsara Albashi na kasa RMAFC ta bayyana cewa a kwai wasu ma’aikatan Babban Bankin Najeriya da albashin su ya dara na Ministocin Kasar.
Shugaban Hukumar, Muhammad Shehu ya ce ba kamar yadda mutane ke zato ba, yan siyasa da dama ba su samun albashin kamar yadda wasu ma’aikatun gwamnati ke samu a Najeriya.
Da yake hira da Kamfanin Dillancin Najeriya a Abuja, Shehu ya ce akwai ma’aikatan gwamnati dake amsar albashi fiye da ministoci da ‘yan majalisa a kasar nan, kuma ma’aikata ne kawai.
Ya ce rabon da aka rawa ‘yan siyasa Albashi tun 2007.
” Ina so in sanar wa ‘yan Najeriya ko albashin shugaban kasa bai kai naira miliyan 1.5 sannan na ministoci bai kan naira miliyan 1 ba.
” Na san wani ma’aikacin babban bankin Najeriya CBN, da ba ma darekta bane amma ya na karbar albashi fiye da minista.
” Akwai ma’aikata a NNPC, NCC da hukumar tashoshin ruwa na Kasar nan da ke amsar albashi fiye da ministoci da yan majalisa har da gwamna ma.
Na san akwai wadanda ke korafin ‘yan majalisa na amsar kudade masu yawa, abinda basu sani ba shine wannan ba alabashi bane, wannan kedin hidima ce ta yau da kullum. Saboda akwai yan siyasa da ke karkashin su, a gundumomin su da sauran hidimomi.
Discussion about this post