Ƙasar Hausa tana yankin sudan ta tsakiya wadda ake kira afirika ta yamma tana tsakanin hamadar sahara daga kudu tana tsakanin chadi da gwiwar kogin kwara.
Haka kuma ƙasar Hausa tana shafi na 15 daga Arewa zuwa layi 18 daga eguator da kuma tsakanin layi na 8 zuwa na 12.
Akwai ra’ayoyin masana akan asalin hausawa ,’amma mafi rinjaye masana sun ta’allaƙa akan wannan batun, Asalin hausawa mutanen Habasha ne wanda a sannu a hankali aka chanja harafin “B” ya dawo “U” Ita kuma “Sh” ta dawo S Maimakon Habasha sai ake cewa hausa.
Harshen hausa kusan shine mafi girma a duk faɗin afirika , sai dai wasu suna gani harshen sawahili yana gaba dashi, a Nigeria akwai kusan harsuna harsuna 450 daban daban amma kusan dukkanninsu sukan yi amfani da harshen hausa a wasu lokutan , domin su sami sauƙin yi mu’amala da junansu kasancewar kowannensu harshen Hausa ya fi sauƙi a tare dasu.
Akwai kusan ƙasashen da harshen hausa ya mamaye cikinsu har ya zama ɗaya daga cikin manyan yarikansu , waɗannann ƙasashen daga cikinsu sun haɗa da , Chadi , Burkina faso , Niger , Congo , Ghana , Togo Sudan , Cameroon , Jamhuriyar Benin , Ƙasar Afirika ta tsakiya , Nigeria , Eriteria asalin wannan ƙasar , ƙasar habasha ce suna da maƙotaka da habasha .
Wani abin sha’awarma a ƙididdigar da aka aiwatar a shekarar 2019 ta nuna cewa masu magana da harshen hausa a faɗin duniya adadinsu ya ta samma kusan miliyan hamsin ba kaɗan(49,900,000).
Saboda irin tasirin da harshen hausa yake da shi a tsakanin harsunan da ake amfani dasu a faɗin duniya yasa har majalisar ɗinkin duniya ta sanyawa harshen hausa rana ta musamman domin tattauna irin cigaban da harshen ya samu da kuma ƙalubalen da al’ummar hausawa da harshensu ke fuskanta . Tarihin wannan ranar yana fara ne daga shekarar 2015, inda a wannan shekarar ne aka fara gudanar da bukukuwan ranar harshen hausa , a ranar 26 ga watan agusta.tun daga wancan lokacin(26-8-2015) aka cigaba da bukukuwa a duk makamanciyar ranar ta kowace shekara, ba’a fara gudanar da bikin ba sai a irin wannan ranar ta cikin shekarar 2018 wato shekara uku da ƙirƙiro wannan rana.
A wannan shekarar wani Ɗan Jaridan( BBC Hausa) wato Abdulbaƙi Jari da wasu masu kishin harshen suka soma bukukuwan ranar hausa a gidan Ɗan Hausa dake nan kano (Hans Vischer ) da wasu ƙasashe a faɗin duniya manufar wannan ranar shi ne ƙalubalantar hausawa domin su fito da sababbin bincike bincike da nazarce nazarce domin haɓɓaka harshen hausa .
Nassarar da aka samu daga shekarar da aka soma gudanar da wannan rana a 2015 ta tabbata da samun haɗin kan al’ummar hausawan duniya a duk inda suka samu kawunansu , wannan yana nuna cewa a duk ƙasar da bahaushe yake zaune ana gudanar da bukukuwan a irin wannnan rana ta 26 ga watan agustan na kowace shekara.
Harshen hausa ya samu tagomashi kasancewarsa a matsayin ɗaya daga cikin harsunan da ake sadar dasu a kafafen yaɗa labarai (Rediyo , talabijin, jaridu ) a ƙasashen hausawa kai har ma ƙasashen da bana hausawa ba.
A yau kusan dukkan gidajen radiyo dake kan zangon fm sun mayar da shirye shiryensu da harshen hausa , kamar gidan rediyo freedom a nan (kano) kusan sune na farko da suka fara shirye- shiryensu da harshen hausa , wanda daga baya sauran gidajen rediyo da suke shirye shiryensu da turanci suka mayar da su harshen hausa . har ma akwai tashar hausa zalla akan zangon fm anan kano mai suna (Arewa rediyo)basa yin amfani da kowanne irin harshe in ba hausa ba. suma gidajen talabijin ba ‘a bar su a baya ba , a wannan ɓangare na bunƙasar harshen hausa , domin suna gabatar da shirye-shiryensu da dama da suka shafi harshen hausa , akwai kamfani dillanci labarai da suma suke samar da jaridu a ɓangaren harshen hausa domin cigaban harshen kamar , jaridar gaskiya tafi kobo ; da jaridar Albishi ;da Alfijir; da Almizan ; da leadership hausa ; da Aminiya wanda kamfani media trust yake bugawa da sauransu .
Ɓangaren ƙasashen da bana hausawa ba kuwa suma sun samar da sashin hausa a kafafen yaɗa labaransu , waɗanda cikin harshen hausa suke gabatar da shirye-shiryensu daga cikinsu irin waɗannan kafofin akwai ,BBC Hausa london; VOA Hausa amurka ; DW Hausa jamus ; RFI Hausa faransa ; CRI Hausa Ghana . da sauran kafofin yaɗa labarai .
Wani abin da Harshen hausa ya samu ɗaukaka dashi shi ne kasancewarsa ɗaya daga cikin manya manyan darusan da ake koyar da shi ko yin nazarinsa a makarantu daban daban dake faɗin duniya alal misali , tun daga matakin karatun firamare harshen hausa yana cikin manya darusan da ake koyawa ɗalibai domin su san ƙa’idoji da kuma yadda yafi kamata ayi amfani da su. Ana koyansa ne tun daga aji ɗaya na firamare har xuwa aji shida , daga nan kuma sai a cigaba da koyansa a ƙaramar makarantar sakandire shekara uku . suma hukumar tsara jarrabawar kammala karatun sakandire wato hukumar shirya jarabawa ta ƙasa NECO da kuma hukumar shirya jarrabawa ta afirika ta yamma WEAC da kuma hukumar shirya jarrabawar makarantun harshen larabci NBAIS da sauransu , ana shiryawa ɗalibai tambayoyin da zasu amsa a wannan darasin.
Su ma manyan jami’oinmu na cikin gida kai har ma da na ƙasashen ƙetare ba’a bar su a baya ba wajen tabbatar da harshe hausa ba matsayin wanda za’ayi nazari a kansa tun daga matakin digiri na farko dana biyu dana uku wato (PHD) Digirin digirgir da kuma matakin shehuntaka (proffesorship) kusan duk jami’oi da suke arewancin nijeriya da sauran ƙasashen afirika kai har ma dana saura sassan duniya suna yin nazarin a harshen haka ne yasa a yau muke da manya manyan masana harshe hausa tare da manazarta a sassan duniya daban daban muna da ɗumbin daktoci a wannan fannin ga kuma shehunnan malamai (Professors) duk dai a wannan ɓangare, kai hatta ma a cikin waɗanda ba hausawa ba akwai irin wɗannan masana da manazarta .
Haka ma ɗaliban da suke yin karatu a ɓangaren harshen Hausa idan sun kammala karatunsu suna samun aiki a gwamnati tarayya , wasu a gwamnatin jaha , wasu a ƙanana hukumomi (local Government).
Bayan kasancewarsa harahen Hausa a matsayin mafi girma a faɗin afirika ta tabbatar da cewa yana ma ɗaya daga cikin manyan haraunan da duniya take tunƙaho da su a tsakanin sauran harsunan duniya baki ɗaya .
Majalisar ɗinkin duniya ta tabbatar da wanna harshe hausa a matsayin na goma sha ɗaya cikin jerin manyan haraunan da ake amfani da su a faɗin duniya wanda adadinsu yakai kusan dubu saba’in da ɗari biyu da hamsi(70,250).
Wani abin sha’awarma shi ne , Gwamnatin saudiyya a lokacin aikin Hajjin bana na shekarar (1443AH–2022AD)Ta zaɓi harshen Hausa domin ya zama ɗaya daga cikin harsuna goma da za a fara fassara huɗuba da su a ranar Arfa.
A shekarun baya ma ita ma Gwmnatin saudiya ta zaɓi wannan harshe a matsayin ɗaya daga cikin harsunan da aka fassara alƙur’ani mai girma da shi saboda yawan musulmin da suke amfani da harahen hausa a faɗin duniya . ita ma hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanya harshen hausa a cikin jerin harsuna guda uku da ta zaɓa domin yaƙi da annobar korona( Covid 19) a nahiyar afirika.
Ana saran harshen hausa zai samu karɓuwa a cikin jerin harsunan da majalisar ɗinkin duniya take amfani dasu , haka ma ƙungiyar haɗin kan Afirika (AU)Da ƙungiya yammacin ƙasashen afirika (ECOWAS) wani cigaba da harshen hausa ya samu ya sake samu shine kamfanin Facebook da Google suna amfani da harshen hausa a manhajarsu , suma manhajar Androin da (IOS) Sun shigar dasu a cikin tsare tsarensu .
Hakan ne yasa nayi nazarin aka wannan Ranar hausa ta duniya , domin nanuwa duniya cewa harshen hausa ya bunƙasa kuma yakai matsayin da za’a ji shi a kowacce nahiya.
Daga Ɗalibin ku Umar Ahmad Rufai Ɗalibi a kwalejin ilimi wato ( Dala College of Education ) kano . sashin kimmiyar harshe (Linguistic).
Discussion about this post