Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero ya fice daga jam’iyyar PDP yau Asabar, 30 ha Satumba.
A wata wasika da ya rubuta da hannun sa ya kuma raba wa manema labarai, tsohon gwamnan ya ce ” Daga yau 30 ga Satumba na fara ce daga jam’iyyar PDP kwatakwata, ba ni ba ita.
Sannan ya kara da cewa tuni har ya mika katun shaidar zama ɗan jam’iyyar a mazaɓar sa dake Ƙaura, cikin birnin Zaria.
A karshe ya yi wa jam’iyyar fatan Alkhairi.
Ramalan Yero ya ɗare kujerar gwamnan Kaduna ne bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Patrick Yakowa.
Sai dai kuma bai samu ya yi tazarce ba a 2015, yayin da tsohon gwamna Nasir El-Rufai na APC ya kada shi a zaɓen gwamnan jihar.
Haka kuma ya yi takarar fidda ɗan gwani na jam’iyyar PDP har sai biya inda Isah Ashiru ya rika kada su.
Sai dai kuma bai faɗi inda zai koma ba a siyasance.
Discussion about this post