A ranar 6 ga Agusta Shugaba Bola Tinubu ya cika kwanaki 100 a kan mulki, lokacin ya na can ya na halartar taron Ƙungiyar G20 a Indiya.
A ranar da aka rantsar da shi ya tari aradun da shugabannin da suka yi mulki kafin shi suka ji tsoron yin gaba-da-gaba da ita, wato cire tallafin fetur. A nan cikin gida da har ma da ƙasashen waje, mulkin Tinubu na tafiya ya na sakin hanya, saboda dishi-dishi ko gani garara-garara da idanun gwamnatin ke yi.
Idan za a ɗora gwamnatin Tinubu kan sikeli, tilas sai an fara auna irin gadangarƙamar da ya gada daga gwamnatin Muhammadu Buhari.
To yanzu dai tallafin fetur ya tafi, ya zama tarihi, kuma kowa ya shiga taitayin sa.
Yayin da irin su Bankin Duniya da IMF ke jinjina wa Tinubu saboda cire tallafin fetur, a nan cikin gida kuwa cirewar ta haddasa gagarimar matsalar ƙuncin rayuwa, raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma barazana ga tattalin arzikin ƙasa.
Ƙarin abin da ruɗa harkoki a cikin ƙasar, shi ne tsarin da gwamnatin Tinubu ta shigo da shi na sakin Naira a kasuwa, domin farashin gwamnati ya yi daidai da na kasuwa. Wannan lamari kuwa bai haifar da ɗa mai ido ba. Domin a ranar Juma’a an canja Dala 1 kan Naira 950. Kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba kenan.
Cire tallafin fetur da sagegeduwar ƙyale Naira ta yi dambe da Dala ba tare da an naɗe mata hannu ba, ya jefa marasa galihu miliyan 133 cikin halin ƙuncin raɗaɗin tsadar rayuwa. Wasu ma zai yi wahala su iya tashi bayan dukan tsiyar da talauci ya yi masu a cikin ɗan ƙanƙanen lokacin nan.
Tsadar rayuwa ta ingiza tsadar kayan abinci da kayan masarufi da farashin kuɗin hawa motar haya, wanda ya nunka har sau uku.
Ire-iren abubuwan da tsare-tsaren da gwamnatin ta shigo da su da kuma abin da ya biyo bayan shigo da tsarin, sun tabbatar da cewa sukuwa aka fara, amma a kan makahon doki.
Saboda ga shi dai a fili, ƙarara ta tabbata cewa ba a yi nasara ba, an gaza wajen cimma dalilin fito da tsare-tsaren, waɗanda aka ce an bijiro da su ne domin a saisaita kasuwa, hada-hada da kuma tattalin arziki.
Ƙoƙarin saisata tattalin ya haifar da yi wa Babban Bankin Najeriya, CBN kwalema, har ta kai an watsar da Gwamnan CBN ɗin, Godwin Emefiele a cikin kwandon shara. A yanzu haka ya na tsare, tare da fuskantar tuhumar zargin danne Naira biliyan 6.7.
A lokaci guda kuma shi ma dakataccen Shugaban EFCC, AbdulRashid Bawa ya na tsare tun ranar 14 Ga Yuni, kuma har yau ba a ce ga laifin sa ba. Ci gaba da tsare shi babban laifi ne da kuma ƙetare iyakar da dokar ƙasa ta gindiya a bisa turbar dimokraɗiyya. Kuma ƙarfa-ƙarfa ce irin ta mulkin Fir’aunanci.
Domin Dokar ACJA ta 2015, cewa ta yi duk tsanani kada a tsare mai laifi fiye da kwanaki 56 ba tare da an gurfanar da shi kotu ba.
Kuɗaɗen Lamunin Noma na ‘Anchor Borrowers Programme’ har Naira tiriliyan 1 da biliyan 100 da CBN ta raba dai da alama sun tafi a gararumar siyasa. Domin wa’adin a karɓo Naira biliyan 577 daga hannun waɗanda ba su biya ba, zuwa ranar 18 Ga Agusta dai ya wuce, kuma shiru ka ke ji.
An kama bankuna biyu sun karkatar da Naira biliyan 10, su ma an ce su maido kuɗaɗen na harajin kwastan.
Wato idan aka dubi gwamnatin Tinubu, za a lura cewa duk wani tsare-tsaren da ta bijiro da shi, ta yi ne domin ƙara samun kuɗaɗen shiga.
Cikin watan Yuni ta tara Naira tiriliyan 1.956, kuma su aka raba wa Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi a cikin Yuli. Wato an samu ƙarin maƙudan kuɗaɗe kenan, idan aka kwatanta da watan Mayu da aka raba Naira biliyan 655.93, sai watan Yuni da aka raba Naira biliyan 785.161.
Amma duk da waɗannan maƙudan kuɗaɗen da gwamnatocin hawa uku suka raba tsakanin su a cikin Yuli, talaka bai ga wani canji a rayuwar sa ba, sai ƙuncin rayuwa, raɗaɗin tsadar rayuwa, tsadar abinci da gagarimar matsalar tsaro.
A daidai lokacin da aka samu waɗannan maƙudan kuɗaɗe, maimakon talaka ya fara ganin sauyi, sai albishir aka yi masa na raba masa abincin tallafi, saboda ƙuncin rayuwa ya jefa miliyoyin mutane cikin sahun mabarata.
Alƙawarin ƙarin albashin da Tinubu ya yi wa ma’aikata zai yi wahala ya cika, domin a yanzu haka shi da kan sa ya ce a duk lokacin da aka kawo masa adadin kuɗaɗen da Najeriya ke kashewa, lamarin na tayar masa da hankali.
Tinubu na nuna damuwa dangane da inda ko yadda zai riƙa samun kuɗaɗen da ake buƙatar kashewa a tafiyar da gwamnati, amma kuma a haka ya kasa taka wa yawan kashe kuɗaɗe barkatai burki. A wannan hali babu wani dalilin naɗa ministoci har 48.
Tallafin kayan abincin da aka fara rabawa bai yi wani tasiri ga jama’a ba. Wasu jihohi ba su fara rabawa ba, a wasu jihohin kuwa an riƙa daka wasoson kayan. Haka kuma akwai ƙaramar hukumar da aka tabbatar cewa an raba wa jama’a ruɓaɓɓiyar masara.
Saboda haka kuma babban abin da ya kamata ya fi damun Tinubu shi ne gagarimar matsalar tsaro a ƙasar nan. Ko kwanaki 40 bai cika a kan mulki ba ƙididdiga ta nuna an kashe mutum 555 a ƙasar nan haka kawai.
Kisan Sojojin Najeriya 36 da kakkaɓo jirgin Sojojin Saman Najeriya wanda ‘yan bindiga su ka yi cikin Agusta, ya nuna akwai jan aiki sosai kan Tinubu a ɓangaren tsaro.
Dalili kenan ma mu ke mamakin abin da zai sa ya naɗa tsohon Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar Ministan Tsaro, shi kuma tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Ƙaramin Ministan Tsaro. Ba a san abin da Tinubu ke son ya cimma a fannin tsaro ba da har ya naɗa su ministocin tsaro.
Ya kamata Tinubu ya girgiza bishiyar tattalin arziki, ‘ya’yan bishiyar su zobo, domin miliyoyin jama’a su samu aikin yi. Wannan shi ne mafita, amma an ƙi gudu, sannan kuma ana daka tsalle a wuri ɗaya, wannan ba hikima ba ce, sai dai a yi ta keto gumi kawai.
Discussion about this post