Sau da yawa ko an yi zaman sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago, a ƙarshe za a ga zaman ba shi da wata fa’ida, domin sun kasa cimma sulhuntawa a tsakanin su.
Rikicin da ya tashi kwanan nan a tsakanin ɓangarorin biyu, shi ne hayaniyar cire tallafin fetur, inda a lokacin taron lamarin ya yi zafi a makon da ya gabata, ta yadda lamarin na neman ya kai ga an shiga yajin aiki na tsawon lokaci a faɗin ƙasar nan.
A ranar Juma’a da ta gabata ce wa’adin kwanaki 21 ɗin da NLC ta bayar cewa ko a biya masu buƙata ko su fantsama yajin aiki, ya cika.
To ga shi ita ma ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta fara dunƙula hannu za ta yi dambe da Gwamnatin Tarayya, yayin da wa’adin makonni biyun da ta bayar ya cika a ranar Alhamis.
Maimakon Gwamnatin Tarayya ta sa himma da ƙwazo wajen aiwatar da wasu alƙawurran da ta yi, sai ta ɓuge wajen haifar da rabuwar kan mambobin ƙungiyoyin ƙwadago.
A ɗaya gefen Ministan Ƙwadago Simon Lalong ya sake nan TUC ta bai wa Gwamnatin Tarayya wani wa’adin makonni biyu domin ta cika alƙawarin da ta ɗaukar wa TUC ɗin.
Kwanan baya NLC ta shirya zanga-zangar kwanaki biyu domin gargaɗi. Abin da ya rage yanzu kawai shi ne su fantsama yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.
Maganar gaskiya dai ita ce yadda Gwamnatin Tarayya ke jan-ƙafa wajen batun ƙarin albashin da ta yi alƙawarin za ta yi, abu ne da ka iya haddasa zanga-zanga mai zafi.
Irin wannan matsalar ake gudu kada ta faru, a duk lokacin da gwamnati ta yi azarɓaɓin bijiro da wani tsari ba tare da yin ƙwaƙƙwaran nazarin alfanu ko rashin alfanu, ko kuma hanyar kawo sauƙi ba.
Gaskiya Shugaba Bola Tinubu ya tafka babban kuskure da ya yi giringiɗishin cire tallafin fetur, a ranar da aka rantsar da shi. Tinubu bai tsaya ya tuntuɓi majiɓinta harkar tattalin arziki ba.
Haka kuma sai daga baya sannan Tinubu ya zauna da shugabannin ƙwadago, inda ya shaida irin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwar da ya tanada, sakamakon cire tallafin fetur.
Amma akwai babbar matsala a ce an bijiro wa jama’a tsadar rayuwa gadan-gadan ta sha kan su, sannan kuma a ce albashin ma’aikata da samun masu harkokin kan su ma nan a wuri ɗaya bai ƙaru da ko sisi ba.
Jama’a sun ƙara burmawa cikin kogin tunani, jin cewa a cikin Agusta sai da Gwamnatin Tinubu ta biya Naira biliyan 169.4 kuɗin tallafin fetur, wai don kada farashin litar fetur ya ƙara tashi sama daga Naira 620.
Haka dai wata jarida ta tabbatar, tare da kafa hujja da bayanan da ta gani cikin Kwafen Jadawalin Kason Kuɗaɗen Gwamnatin (FAAC). Wannan lamari lallai abin dubawa ne.
Ƙarin tashin hankali kuma shi ne yadda darajar Naira ta sakwarkwace baki ɗaya, ta yadda a yanzu dala ɗaya tilo har ta haura Naira 1,000 a kasuwar ‘yan canji.
Kwana-kwanan nan kuma ƙididdiga daga Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanan Fatara da Talauci ta ce tsadar rayuwa da tsayar kayan abinci ya tashi sama da kashi 25.8 bisa 100. Haka farashin hawa motocin haya ya nunka, ya ƙara ma ruɓanyawa a wasu wuraren.
Su kuma NLC da TUC ƙarin kashi 200 zuwa kashi 300 na albashi su ke buƙata. Sannan kuma su na so a gaggauta gyara matatun fetur ɗin ƙasar nan, domin a rage tsadar fetur, kuma a daina sayo shi daga waje. Da dai sauran buƙatu masu muhimmanci.
Ya kamata dai gwamnati ta san cewa mutane fa na fama da matsananciyar yunwa. Kuma da dama kan iya fita hayyacin su su shiga tafka ɓarna don neman abin saka wa bakin salati.
A yankuna da dama ana tare motoci masu ɗauke da kayan abinci ana daka wasoso. Don haka ko ba a ƙara fayyace wa gwamnati komai ba, a haka kaɗai ta san talakawa na cikin mawuyacin hali.
Magance matsalar da gaggawa zai hana talakawa fusata har su ma su jefa ƙasar cikin wani mawuyacin halin da ya fi na yanzu.
Discussion about this post