‘Yan ta’adda sun nuna tantagaryar zafin rai, taurin kai zunzurutun rashin tsoron yin taho-mu-gama da mutuwa, inda su ka kai wa Sojojin Najeriya mumnunan harin kwanton ɓauna, cikin watan jiya a Jihar Neja. Ƙarin abin haushi da takaicin kuma shi ne ƙumumuwar da suka yi har su ka kakkaɓo jirgin Sojojin Saman Najeriya, wanda aka tura domin kwaso sojojin da ‘yan ta’adda ɗin su ka jikkata, tare da kashe soja 36 a hare-haren biyu.
Ba fa wannan ne karo na farko da aka salwantar da rayukan Sojojin Najeriya a irin wannan yanayin ba. Wannan bala’i dai ya zama wajibi ya zama babban darasi ga sabuwar gwamnati, domin ta san cewa akwai babban ƙalubale a gaban ta.
Sojojin da aka kashe ɗin dai an tura su ne yaƙin kakkaɓe ‘yan ta’adda a Kundu, cikin Ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja. Maimakon su kakkaɓo ‘yan ta’addar, sai ‘yan ta’adda ɗin su ka yi masu kwanton-ɓauna, suka kakkaɓe su. Wataƙila wannan abin takaici akwai hannun wasu marasa kishin jami’an tsaro a lamarin.
A harin kwanton-ɓauna dai an halaka soja 14, aka jikkata bakwai. Sai kuma jirgin da ‘yan bindiga su ka kakkaɓo, shi kuma a lokacin ya na ɗauke da waɗanda aka jikkata da gawarwakin waɗanda aka kashe. Nan take gogarman ɗan ta’adda, wani ƙaton ƙauye wai shi Dogo Giɗe, ya ce shi ke da alhakin kakkaɓo jirgin, a wani bidiyon da suka watsa duniya ta gani.
Wannan la’anannen ɗan iska dai abu mafi alheri shi ne a kakkaɓe shi, a shafe shi daga doron ƙasa shi da sauran dandazon ‘yan ta’addar da ke tare da shi a cikin daji.
‘Yanzu ‘yan ta’adda sun kafa sansani mai ƙarfin gaske a Jihar Neja, su na guje wa hare-haren da Sojojin Najeriya ke kai masu ba ƙaƙƙautawa a Arewa maso Gabas.
Waɗannan ‘yan ta’adda sun miƙe ƙafa a dajin Jihar Neja, saboda faɗin yawan daji a jihar, sannan kuma ga shi Neja ta haɗa kan iyaka da Jihar Zamfara, Kaduna, Katsina da Sokoto, waɗanda ‘yan bindigar su na kwarara cikin Jihar Neja kan su tsaye.
Ire-iren waɗannan gaggan ‘yan iska ne suka tsallaka har Kuje a Abuja, su ka karya kurkuku, su ka kuɓutar da kwamandojin Boko Haram 60, kuma suka saki ɗaurarru 800. Su ne dai su ka kashe Zaratan Sojoji Dogaran Shugaban Ƙasa a Bwari, kusa da Abuja a cikin 2022.
Shugaba Bola Tinubu zai riƙa kasancewa ya na kwana, ya na tashi a cikin mafarki, idan ya ce ta irin hanyar da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bi, shi ma ita zai bi don ya daƙile ‘yan bindiga.
Baya ga irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnatin Buhari ta narkas wajen sayen makamai, jiragen yaƙi, shawarwarin ƙwararru daga manyan ƙasashe, lamarin bai haifar da ɗa mai ido ba.
Sai dai a wani ɓangaren, an ji yadda jami’an leƙen asiri suka bankaɗo yadda wasu kamfanoni 123 da ‘yan canji 33 suka riƙa ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, kamar yadda Ministan Yaɗa Labarai na lokacin, Lai Mohammed ya bayyana.
Shi ma Ministan Shari’a na lokacin, Abubakar Malami ya fito ya ce za a gaggauta gurfanar da su a gaban shari’a, domin su girbi baƙar aniyar da su ka shuka. Amma abin mamaki, al’ajabi da takaici, har Buhari ya sauka ba a hukunta su ba.
Ba a banza ba a lokacin da gwamnatin Buhari ke jan-ƙafa ta na ƙoƙarin mantawa da batun hukunta masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’addar, Babban Lauya Femi Falana (SAN), ya fito ya zargi Abubakar Malami da “kange masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, ya ƙi bari a hukunta su, duk kuwa da ƙwararan hujjojin da masu bincike su ka gabatar.”
Irin wannan sakarci, shashanci, sakaci, shirme da shiririta bai kamata a ce ya fito daga ƙasar da ‘yan ta’adda ke ƙoƙarin durƙusarwa ba.
Haɗa kan da aka yi da Amurka da UAE, ya samar da nasarar kama masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda har su 400, cikin 2021, waɗanda ke ƙulla mugun aiki a Najeriya.
Yayin da Najeriya ta yi wasarere daga hukunta waɗanda aka kama a nan ƙasar, ita kuwa UAE sai ta gaggauta hukunta ‘yan Najeriya ɗin da ta kama su na aiko wa ‘yan ta’adda kuɗaɗe zuwa cikin Najeriya.
Waɗanda ta ɗaure sun haɗa da Abubakar Ado Musa, Salihu Yusuf Adamu, Bashir Ali Yusuf, Mohammed Ibrahim Isa, Ibrahim Ali Alhassan da Surajo Abubakar Mohammed.
An kama su da laifin turo wa ‘yan ta’adda Dala 782,000 daga Dubai zuwa Najeriya. Aka ɗaure Salihu Adamu rai-da-rai, Surajo da sauran kuma kowane ɗaurin shekaru goma-goma a kurkuku.
Ya kamata Shugaba Tinubu ya karkaɗe wannan fayil, ya ce a gaggauta hukunta waɗanda aka kama a nan Najeriya.
Amma idan ba a yi haka ba, to ya nuna asarar biliyoyin kuɗaɗe kawai ake yi ma Daloli da sunan yaƙi da Boko Haram da ‘yan bindiga, ga babbar asarar kisan fiye da mutum miliyan 100,000 na fararen hula da sojoji.
Amma ba za a iya yin nasarar kakkaɓe ‘yan ta’adda ba, a lokacin da ake neman taimakon ƙasashen waje, a cikin gida kuma ba a hukunta masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda ɗin.
Irin wannan munafircin ke haifar mana asarar ɗimbin sojoji, tare da sare masu guyawun da dama sun daɗe su na haƙilon wannan yaƙi da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
PREMIUM TIMES ta yi amanna da cewa kisan Sojojin Najeriya da ‘yan ta’adda ke yi ya yi yawan da tilas a tashi tsaye a magance matsalar. A datse hanyar da ‘yan ta’adda ke samun kuɗi, tamkar zare masu rai ne.
Amma a ƙyale jaki ana dukan taiki a yaƙi da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, to tamkar ci gaba ne da tura sojojin mu haka kawai ƙartin banza ‘yan ta’adda na kashe su.
Ya zama tilas gwamnati ta kashe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, domin ta raya Sojojin Najeriya.
Discussion about this post