Rundunar NSCDC reshen jihar Kaduna a ranar Talata ta dauki mutum 7 aiki daga cikin iyalan jami’an ta da ‘yan bindiga suka kashe.
Idan ba a ranar 14 ga Janairu ‘yan bindiga sun yi wa dakarun rundunar bakwai kisan gilla a karamar hukumar Birnin Gwari.
Kwamandan rundunar Idris Adah wanda ya gabatar wa ƴan uwan mamatan da aka ɗauka aika takardar ɗaukan aikin ya ce yin haka cika alkawari ne da Shugaban hukumar Ahmed Audi ya yi wa iyalan jami’an da aka kashe.
Alhaji Baba Audi-Landan wanda ya yi magana a madadin wadanda aka dauka aikin ya mika godiyarsa sannan ya ce aikin zai taimaka wa iyalai da sukan su waɗanda aka ɗauka.
Discussion about this post