Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta Kasa da ta Jiha da ke Kano ta kori Dankawu Idris na jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP) bisa samunsa da laifin yin jabun takardar shaidar kammala sakandare.
Honarabul Idris yana wakiltar mazabar tarayya ta Kumbotso ta jihar Kano, a majalisar wakilai.
Daga nan ne Alkalin kotun I. Chima ya ayyana Mannir Danagundi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu.
Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, alkali kotun ya ce takardar shaidar kammala jarabawar WAEC wanda Idris, ya bayar jabu ce ba.
Daga nan ne kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ba dan takarar jam’iyyar APC, Dan-agundi, takardar shaidar cin zabe.
Jam’iyyar NNPP ta rasa kujerun yan majalisa uku kenan a kotu.
Discussion about this post