Hukumar NDLEA ta kama muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 685 sannan ta ragargaza wuraren siyar da kwayoyi da mahaɗar yan iska 13 a jihar Kaduna.
Shugaban hukumar Ibrahim Barji ya sanar da haka ranar Lahadi yana mai cewa jami’an hukumar sun yi wannan kame ne a watan Agusta.
Barji ya ce dakarun hukumar sun kama mutane 86 dake da alaka da sha ko safarar muggan kwayoyi a jihar inda a cikinsu akwai maza 83 da mata uku.
Ya ce dakarun sun kama muggan kwayoyi da suka hada da ganyen wiwi 650.690 kg, hodar ibilis 0.004 kg, Methamphetamine 0.197 kg, Tramadol 9.336 kg da wasu haramtattun kwayoyin da suka kai nauyin 24.949 kg.
Askarawan sun kama makamai da suka hada da harsasai guda 100, karamar bindiga mai lamba 73.1×19, karamar bindiga kirar hannu da sauransu.
Barji ya kuma ce dakarun sun ragargaza wuraren siyar da muggan kwayoyi a Tirkaniya, Kantin Kwari garage, Badarawa, Filin Minister, Mangarori, Kafanchan, Unguwar Gimbiya, Kauru, Birnin Yero, Narayi, Unguwar Gwari, Hayin Na’iya da Hayin Dan Mani.
Ya Yi kira ga mutane da su hada kai da hukumar domin yakar Sha da safarar muggan kwayoyi a faɗin jihar.
Barji ya ce taimaka wa hukumar da bayanan da za su taimaka wajen samun sauƙi a aikinsu zai taimaka wajen inganta matakan yaki da matsalar a kasar nan.
Discussion about this post