Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma tsohon Ministan Ilmi, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa zai yi wahalar gaske kafin a samu jajirtaccen shugaban da zai iya rage maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen tafiyarwa ko gudanar da aikin gwamnati a Najeriya.
Shekarau wanda ya yi Sanata daga 2019 zuwa 2023, ya ce ɗaya daga cikin manyan dalilan rashin yiwuwar rage facaka da kuɗaɗen, shi ne saboda waɗanda nauyin ragewar ke wuyan su, su ne mafi amfana. Saboda haka zai yi wahalar gaske su aiwatar da ragewar.
Da ya ke tsefe wannan gagarimar matsala, Shekarau ya ce akwai mambobi 469 a Majalisar Ƙasa, akwai kwamitoci 103 a majalisa. Sannan kuma akwai ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya fiye da 500.
Shekarau ya ce wasu hukumomi ko cibiyoyin gwamnati maimaitawa ce ko kuma irin aikin su ɗaya da wasu hukumomin.
Ya ce don haka tunda kwamitocin majalisa ke duba su, zai yi wahala su amince su rage su, domin su ke amfana da su.
Sanata Shekarau ya yi wannan tsinkayen ne a lokacin da ya ke jawabi, a matsayin sa na babban baƙo mai jawabi, a Taron Shekara-shekara na Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi na Najeriya (MSSN) na Shiyyar B, wanda aka yi a Osogbo, Jihar Osun, a ƙarshen makon da ya gabata.
Kakakin Yaɗa Labaran Shekarau ne, Sule Ya’u Sule yaɗa jawabin a kafar sada zumunta, wadda ake sanar da manema labarai abubuwan da su ka shafi tsohon Gwamnan Kano, Shekarau.
Sanatan wanda aka fi sani da laƙabin Malam, ya ce za a ɗauki lokaci ko kuma har sai ranar da aka samu jajirtaccen shugaban ƙasa, kafin a kai ga lokacin rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.
“To wa ku ke ganin zai gyara dokokin? Idan gyara ne dai to daga Majalisa ake farawa. Kuma tunanin ‘yan majalisa 469 za su amince su zauna, su soke majalisa ɗaya su bar ɗaya?
“Ai idan ba tsarin alƙiblar dimokraɗiyyar aka canja ba, babu yadda za a yi a rage yawan kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tafiyar da gwamnati.”
Shekarau ya buga misali da Ma’aikatar Harkokin Ilmi, inda ya yi minista, ya ce akwai cibiyoyi 23 a ƙarƙashin ma’aikatar.
“Dimokraɗiyyar da sojoji su ka ƙaƙaba mana, tare da ɗora mu a kan ta, mai tsadar gaske ce. Akwai kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tafiyar da ita.
“Kasancewar na yi Sanata, na samu damar ganin yadda ake facaka da kuɗaɗen gwamnati. Dalili kenan ni dai a nawa ra’ayin, ba mu buƙatar Majalisa guda biyu mai mutum har 469.
“Kun ga a Majalisar Dattawa akwai kwamitoci 73. Aƙalla kowane sanata ya na cikin kwamitoci biyar, wasu ma har bakwai ko ma takwas.
“Su ma mambobin Majalisar Wakilai ta Ƙasa na da kwamitocin su 130. Idan wannan hukuma ta je Majalisar Dattawa ta kare kasafin ta, irin abin da aka yi ne dai za a sake maimaitawa idan sun je Majalisar Tarayya.
“Muna da hukumomi fiye da 500 a ƙarƙashin gwamnatin tarayya, kuma yawancin su ayyukan su iri ɗaya ne. “Misali, mene ne ya bambanta aikin EFCC, ICPC da CCB. Duk aiki ɗaya su ke tuma tsalle su ne dira akai, a wuri ɗaya.” Inji Shekarau
Discussion about this post