Mataimakin Shugaban Kashin Shettima, ya bayyana cewa Najeriya fa a jaywalgwale ta ke, don haka akwai jan aiki haiƙan a wuyan Kwamitin Bunƙasa Tattalin Arziki da Sauya Tsarin Haraji na Shugaban Ƙasa, ya bijiro da hanyoyin inganta tattalin arzikin Najeriya.
“Na yi amanna cewa za ku fito da daftarin da za a shata gwadaben hawa tudun-mun-tsira. Saboda muna cikin wani mawuyacin hali. Najeriya da jagwalgwale ta ke.
“Amma dai ni ina da yaƙinin cewa tawagar ku na da basirar za ku cimma muradun inganta tattalin arzikin Najeriya.
“Najeriya ƙasaitacciyar ƙasa ce wadda ta yi rashin sa’ar nagartaccen shugabanci. Sannan kuma ga sauran ƙalubale da dama da suka dabaibaye ta.”
Shettima ya yi wannan horo ga kwamitin a makon da ya gabata, lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin Kwamitin Sake Fasalin Tsarin Haraji, bisa jagorancin shugaban kwamitin, mai suna Taiwo Oyedele.
Shettima ya karɓi baƙuncin maziyartan sa ɗin a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Ya ce ya na da yaƙinin cewa za su fito da ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bunƙasa haraji, domin a cewa su ne ƙashin bayan ci gaban tattalin arzikin kowace ƙasa.
Ya ce tsarin tasarifin kuɗaɗe da haraji su ne ruhin tattalin arziki. Don haka ya hori ‘yan kwamitin su fito da shawarwarin da duk suka san gwamnati za ta iya aiwatarwa, bisa yin la’akari da halin matsin lambar tattalin arzikin da ake fuskanta a Najeriya.
“Za mu fi maida hankali kan samar da kuɗaɗen shiga a cikin gida, musamman idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu, inda hatta manyan ƙasashe masu arziki ma su na ji a jikin su.”
Shettima ya jinjina wa kwamitin tare da cewa dukkan ‘yan kwamitin ƙwararrun masana ne, gogaggu kuma masu kaifin basira.
Discussion about this post