Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a iya sanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi, ba san ashe shi ma ya iya yin bushasha da kuɗi fiye da yadda ake tsammani.
A hira da Olusegun Obasanjo ya yi ada Jaridar The Cable, Obasanjo ya ce zai yi wuya kasahen da ke bin Najeriya bashin kuɗi su yafe mata kamar yadda aka yi a lokacin mulkin sa ganin yadda aka kashe kuɗi na babu gaira babu dalili a lokacin wannan mulki.
” Tinubu ya ce a kwanan baya wai ba zai yiwu ace wai zai rika kashe kashi 90 cikin 100 na kudin shiga na kasa ba wajen biyan basuka.
” A lokacin ina mulki, ban kashe kashi 90% na kuɗaɗen kasa ba. Kuna ganin yanzu akwai wanda zai yafe wa Najeriya basukan da yake binta? Buhari kashe kuɗi ya rika yi zamanin mulkin sa ko kan gado babu. Na sani Buhari bai san yadda za a gyara kasa da tattalin arzikin ta ba, amma bam san ashe tantirin ɗan bindiga ne ashe. Yana kashe kuɗi na babu-gaira-babu dalili. Na saka haka a littafi na, amma maganan barnata kudi, ban saka ba.
Da yake magana game da matatun man kasar nan, Obasanjo ya ce wahalar banza ce za a yi ta yi idan aka wai har yanzu maganan gyaran su ake yi.
Ba za su gyaru ba, in dai suna karkashin gwamnati ne. Ƴan kasuwa ne kawai za su iya ruke su su gyara su sannansu tada su su fara aiki.
Na yi haka, amma gwamnatin da ta gaje ni ta maida su karkashin gwamnati. Amma gaskiyar magana, ba za su yi aiki ba indai karkashin gwamnati suke, gwamnati ba su iya rike su yanzu. Gaskiyar magana ke nan.
Discussion about this post