Wani direban A Daidaita Sahu, wato Keke NAPEP, mai suna Auwalu Salisu, ya maida Naira miliyan 12 da wasu fasinjoji su ka manta a cikin keken sa.
Lamarin ya faru a ranar Alhamis, kamar yadda Gidan Radiyon Arewa Radio ya ruwaito.
Auwalu wanda ya tsinci kuɗin ya nemi waɗanda su ka sauka su ka manta kuɗin a cikin wata jaka, amma bai gan su ba. Washegari sai ya ji sanarwa a Arewa Radio ana cigiyar mai A Daidaita Sahu ɗin da aka manta kuɗin a cikin babur ɗin sa.
Masu kuɗin dai sun ba shi tukuicin ladar tsinuwa har Naira 400,000, tare da yi masa godiya da sa masa albarka.
Salisu ya bayyana cewa ya maida kuɗin ga mai su, saboda ba haƙƙin sa ba ne.
Ya ce lallai kuɗin su na da yawa, to amma kuma ba za su amfana masa da komai na alheri a duniya da lahira ba, saboda ba shi ne ya sha wahala, ya yi gumin tara kuɗin ba.
Ya ce, “idan ma na riƙe kuɗin, Allah ba zai yi masu albarka a hannu na ba. Saboda haƙƙin wani ne, ba haƙƙi na ba ne.”
Da ya ke bayyana yadda lamarin ya faru, Salisu ya ce, “Na ɗauko su daga Badawa na kai su kusa da ‘Yankaba. Su ka sauka, muka manta da jaka da kuɗi a cikin ta. Ban lura da jakar ba sai daga baya.
“Na taɓa ta, na ji kuɗi a ciki masu yawa, bandir-bandir. Kuma ina buɗewa sai na ga kuɗi a ciki. Nan fa na garzaya gida, na nuna wa mahaifiya ta. Ita kuma ta ce na nuna wa mahaifi na.
“Daga nan sai mahaifi na ya kira ɗan uwan sa. Muka ɗunguma zuwa inda na ajiye su, amma ba mu gan su ba.
“Na koma na ce wa iyaye na ban gan su ba. Sai su ka adana kuɗin kafin a ji an yi cibiya a gidan rediyo.
“To daga baya sai na ji an yi cigiya a Arewa Radio. Na ɗauki lambobin da aka ce a kira. Na yi ta kiran ta farko ba a ɗauka ba. Ina kiran ta biyu, sai aka ɗauka.
“Su ka tambayi inda za su je su same ni. Na ce masu mu haɗu a Arewa Radio, ƙarfe 10 na safe.” Inji Salisu, wanda aka gwangwaje da tukuicin Naira 400,000.
Abokin wanda ya manta kuɗin mai suna Musa Hassan, ya yaba wa direban sosai, musamman yadda ya nuna tsoron Allah har ya maida masu kuɗin, duk kuwa da cewa iyayen sa na fama da raɗaɗin tsadar rayuwa.
Mai kuɗin dai ɗan asalin ƙasar Chadi ne, kuma ya yi ta rusa kuka saboda murna, lokacin da ake tattaunawa da abokin na sa Bahaushe.
Kuɗin dai saifa ce ta adadin Naira miliyan 10, sai kuma Naira miliyan 2.9.
Discussion about this post