Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa mutum 7,202 sun kamu da cutar diphtheria sannan cutar ta yi ajalin mutum 453 a jihohi 18 a ƙasar.
Wannan sanarwa na kunshe a wata takarda dake dauke da sa hannun hukumar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya, hukumar NCDC, hukumar NPHCDA da dai sauran su da aka fitar ranar Litinin.
Gwamnati ta ce an gano mutum 7,202 da suka kamu da cutar bayan gwajin cutar da aka yi wa mutum 11,587 da ake zaton sun kamu da cutar daga kananan hukumomi 105 dake jihohi 18.
Zuwa yanzu jihar Kano na daga cikin jihohin da cutar ta fi yin tsanani. Akalla mutum 6,185 ne suka kamu da cutar a jihar.
Sauran jihohin da cutar ta bullo sun hada da Yobe (640), Katsina (213), Borno (95), Kaduna (16), Jigawa (14), Bauchi (8), Legas (8), FCT (5), Gombe (5), Osun (3), Sokoto (3), Niger (2), Cross River (1), Enugu (1), Imo (1), Nasarawa (1) da Zamfara (1).
Gwamnati ta kuma ce mutum 5,299 daga cikin 7,202 din da suka kamu da cutar yara kanana ne masu shekara 1 zuwa 14 sannan masu shekara biyar zuwa 14 sun fi yawa daga cikin su.
Cutar Diphtheria
Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.
Cutar ya fi kama yara kananan da manyan mutane musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.
Kamuwa da cutar
Ana iya kamuwa da cutar idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.
Idan mai dauke da cutar ya Yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.
Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hankichi da sauran su.
Mutanen da suka fi yawan kamuwa da cutar
Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.
Discussion about this post