Wasu ‘yan bindiga sun datse kan jigon jam’iyyar LP a Jihar Abiya.
Mamacin mai suna Zachary Maduka, shi ne Daraktan Kamfen na LP a zaɓen 2023. An guntule masa kai ne a ranar Laraba da dare, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.
Maduka, wanda dattijo ne mai shekaru 70, ɗan asalin garin Akpukpa ne a cikin Ƙaramar Hukumar Isuikwuato.
Majiyoyi daban-daban sun shaida wa wannan jarida cewa maharan kimanin su 10 kowane ɗauke da bindiga da adduna, su ka afka cikin garin da su ka iske shi, suka danƙara masa harbi a mashayar giya cikin Amelechi, wani ƙauye kusa da Akpukpa.
“Suka sa adda suka guntule masa kai, kuma suka arce da ƙiren kan.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES, amma ta roƙi a sakaya sunan ta.
Kafin kashe shi, mamacin shi ne Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Al’ummar Uturu a yankin na su.
Kakakin ‘Yan Sandan Abiya, Maureen Chinaka, ta tabbatar da afkuwar kisan, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.
Ta ce sun garzaya sun ɗauko gangar jikin mamacin, kuma su na nan su na bincike da farautar makasan.
Discussion about this post