Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysom Wike ya amince da bai wa wasu masu filaye 189 wa’adin ginawa cikin watanni uku kacal, ko kuma ya ƙwace su daga hannun su, a bai wa waɗanda ke da aniyar ginawa cikin gaggawa.
Daraktan Yaɗa Labarai na FCT Abuja, Muhammad Sule ne ya bayyana haka ranar Lahadi.
Ya ce masu filayen sun je sun karɓi kwafe-kwafen takardun sharuɗɗa da ƙa’idojin gini a Abuja, amma har yau ba su fara ginin ba.
Ya ce masu filayen waɗanda suka haɗa da ɗaiɗaikun mutane da kuma kamfanoni, sun nuna alamar niyyar ginawa tunda har sun karɓi ƙa’idojin gini, shi ya sa aka yi masu alfarmar ginawa a cikin watanni uku, maimakon a ƙwace kai-tsaye.
Sule ya ce su ma ma’aikatun gwamnati masu filayen da ba su kai ga ginawa ba, ana umartar su da su gaggauta ginawa cikin watanni uku, ko kuma su ɗin ma a ƙwace su, domin rashin gina fili karya doka ce a Abuja.
“Waɗannan filaye 189 ba a ƙwace su daga hannun masu ba, saboda sun nuna aniyar fara ginawa, domin har kowanen su ya takardun ƙa’idojin fara gina fili a FCT Abuja.
Daga nan Wike ya umarci duk ma wani da aka bai wa fili, to ya fara ginawa kawai, kada ya bari gwamnati ta ƙwace ta bai wa mai iya ginawa.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da su ka wuce Wike ya soke lasisin satifiket na haƙƙin mallakar filaye 165 a Abuja, ciki har da na manyan mutane da dama.
Discussion about this post