Wata matar aure Ruqayya Mukhtar ta garzaya kotun Shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna inda ta nemi kotu ta raba auren ta da mijinta Nasiru Hamza saboda kaurace mata da ya yi.
Ruqayya ta ce ba za ta ci gaba da zama da Hamza ba saboda ya kaurace mata na tsawon shekaru biyu.
Bayan ƙaurace mata da yake yi Rukayya ta ce yaka rika jibgar ta haka kawai idan ya bushi iska.
Amma kuma Hamza ya karyata duk abin da Ruqayya ta fadi yana mai cewa yana kokari matuka wajen kula da matarsa.
“ Saboda tsananin nema domin ciyar da iyali na wata rana da daddare na ke dawo wa kuma na gaji shi yasa ban iya komai sai barci.
“Duk da haka ina kokari wajen biya mata bukata amma ita bata gamsuwa, a yi ta buga harka ta ke so.
” Da na lura da haka sau dayawa na kan bata hakuri ta ɗan ɗaga min kafa in huta, inndan samu karfi, amma ta yi kememe, ita ba haka ba.
Hamza ya faɗi cewa tun da ya auri Ruqayya bai taba dukan ta ba kuma bai taba zaginta ba.
Alkalin kotun Anass Khalifa ya tambayi Ruqayya ko tana da shaidan da za ta iya gabatar wa ta ce tana da shi.
Khalifa ya dage shari’ar zuwa ranar 5 ga Satumba domin Ruqayya ta gabatar da shaidan ta a zama na gaba da kotun za ta yi.
Discussion about this post