A ranar Litinin ce Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayar da umurnin ɗaukar ‘yan sa-kai a matsayin ƙari ga ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi don magance matsalar tsaro.
“Ɗaukar ‘yan sa-kai na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna a zaman majalisar zartaswar Jihar Zamfara, wanda Gwamna Lawal ɗin ya jagoranta.”
Wata sanarwar da Mai Magana da Yawun gwamnan, Sulaiman Idris ya fitar, wadda ya wallafa a shafin sa na Facebook, ta ce an gudanar da wannan zama na Majalisar Zartaswar ne a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara, da ke Gusau.
Ya ƙara da cewa, har wayau, a wurin taron majalisar ta bada umurnin a gina sabbin ajujuwan karatu, tare da sabunta wasu a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar.
Ya ce: “A yunƙurin sa na ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro, Gwamna Dauda Lawal ya aminta da ɗaukar ‘yan sa-kai a dukkanin ƙananan hukumomin Zamfara.
“Duk dai a zaman majalisar zartaswar da ya jagoranta, ya aminta da ginawa, tare da sabunta ajujuwan karatu a faɗin ƙananan hukumomin.
“Za a ɗauki ‘yan sa-kai 300 a kowacce ƙaramar hukuma ta jihar, waɗanda za a bacsu horaswar da ta dace, domin su ci gaba da taimaka wa soji da ‘yan sanda kan yaƙi da ‘yan ta’adda.
“Majalisar ta aminta da gina sabbi tare da sabunta ajujuwan karatu guda 49 a Gusau, 11 a Anka, 15 a Bakura, 8 a Bukkuyum, 14 a Birnin Magaji, 8 a Bunguɗu, 8 a Gummi, 19 a Kauran Namoda, 8 a Maru, 11 a Maradun, 42 a Shinkafi, 8 a Talata Mafara, 27 a Tsafe da kuma guda 11 a Zurmi.”
Discussion about this post