Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda ‘yan bindiga ke ƙara himmar kai munanan hare-hare a jihar sa.
Mohammed ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta kai wa Jihar Bauchi ɗauki, ya na mai cewa ‘yan bindigar su na ci gaba da kai wa mazauna yankunan karkara hare-hare da garkuwa, alhali waɗanda ake kai wa hare-haren ba su iya kare kan su.
Gwamna Bala Mohammed ya roƙi a kai wa Bauchi ɗauki ne daga Gwamnatin Tarayya, a lokacin da ya ke ganawa da sarakunan gargajiya na Jihar Bauchi, ranar Laraba, a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.
Ya shaida wa sarakunan gargajiyar cewa ‘yan ta’adda gungu-gungu daga jihohin da ke maƙautaka da Bauchi na ci gaba da yin hijira zuwa jihar Bauchi a cikin dazuka.
Ya ce hijirar ta su ta na zuwa ne a daidai lokacin da Sojojin Najeriya ke ci gaba da kwankwatsar su ba ji, ba gani.
“‘Yan ta’adda na ci gaba da yin kaka-gida a dazukan Bauchi, su na tserewa daga lufuden wutar da Sojojin Najeriya ke yi masu a sansanonin su.
Ya ce sun shigo cikin dazukan Bauchi, sun yi kaka-gidan da su ka zama alaƙaƙsi ga al’ummar Jihar Bauchi, musamman ma mazauna yankunan karkara.
Gwamnan ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da faɗin dajin da Bauchi ke da shi, ta ƙoƙarta wajen kakkaɓe ‘yan bindigar, ta yi masu luguden wuta, kamar yadda take ragargazar su a sauran jihohin da ke fama da ‘yan bindiga.
Ya shaida wa sarakunan garzajiya cewa, ya kafa Ma’aikatar Kula da Harkokin Tsaro wadda ke da kwamishinan ta sukutum.
Ya kuma gargaɗi sarakunan cewa su tabbatar da su na sanin baƙin da ke zuwa.
Ya ce kuma duk basaraken da aka kama ya na haɗin baki da maɓarnata, to zai tsige masa rawani ba tare da ɓata lokaci ba.
Discussion about this post