Ƙarin kuɗin karatu a da jami’o’in Gwamnatin Tarayya su ka yi, a daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa a Najeriya, ya fara samun tirjiya, yayin da ɗalibai a Jami’ar Jos su ka fita zanga-zangar rashin yarda da ƙarin.
Ɗaliban Jami’ar Jos a Jihar Filato sun hau titi su na zanga-zangar rashin amincewa da ƙarin kuɗin makaranta da Jami’o’in Gwamnatin Tarayya su ka yi.
Da farko dai ɗaliban sun taru ne a ƙofar shiga harabar makarantar su ka riƙa waƙoƙin rashin amincewa da ƙarin kuɗin makaranta. Sun riƙa watsa bidiyon zanga-zangar a shafukan sada zumunta, wato soshiyal midiya.
Sun kuma riƙa ɗaga kwalaye masu ɗauke da rubuce-rubuce daban-daban, kamar: “A Ƙyale Talaka Ya Yi Numfashi”, “Digiri Mu Ke Nema Ba Bashi Ba”, da sauran su kalamai masu kaushi.
A cikin watan jiya ne makarantar ya yi ƙarin da ya nunka yadda ake biya har sau kashi 150.
Da farko Jami’ar Jos ta ƙara kuɗin shiga kowane sabuwar shekara zuwa Naira 200,000. Amma kiki-kaka ɗin da aka riƙa yi tsakanin ɗalibai, jama’a ya sa aka rage kuɗin, kamar yadda Rajistara ɗin su, Abdullahi Abdullahi ya bayyana.
Wani ɗan aji na 400 ya ce kuɗin da ya ke biya sun tashi daga N45,000 zuwa N110,000.
Wani ɗan aji na 300 cewa ya yi an ce sai ya biya N105,000.
Jami’o’i da dama sun ƙara kuɗaɗe, kuma har yanzu ana ci gaba da kiki-kaka.
A ɗaya gefen kuma, iyaye da dama sun kasa biya wa ‘ya’yan su kuɗin tafiya jami’a, musamman waɗanda za su fara shekarar farko ta digiri kan fannonin kimiyya daban-daban.
Wani magidanci a unguwar Karkasara a Kano, ya umarci ‘ya’yan sa uku su haƙura da tafiya Jami’ar Bayero, saboda tsadar kuɗin rajistar fara karatun digiri.
Discussion about this post