Jami’o’i biyu a Najeriya sun yi zarra, yayin da su ka shiga cikin mashahurai kuma zaƙaƙuran jami’o’i 1000 da ake tinƙaho da su a duniya cikin zangon 2024.
Jami’o’in su ne Covenant University da ke Jihar Ogun da kuma University of Ibadan.
Su biyun su na cikin jerin Mashahuran Jami’o’i 1000 na Duniya, wanda Mujallar Times ta fitar a ranar Laraba, wato Times High Education (THE).
Su biyun sun samu kutsawa a tsakanin na 800 zuwa na 1000.
Sauran jami’o’in Najeriya da ke rufa masu baya sun haɗa da Federal University of Technology da ke Akure da kuma University of Lagos, waɗanda suka samu kutsawa a wajen na 1001 zuwa 1200.
Jami’ar Bayero University, Kano ta fita kunya, inda ta zo ta 1201, University of Ilorin ta 1501, sai kuma University of Nsukka, da ke Enugu, wadda ita ma ta na wajen ta 1501.
A wannan shekara, an bi diddigin jami’o’in duniya har guda 2,673, inda guda 1,904 kaɗai su ka samu tsallake siraɗi daga ƙasashe 108 daban-daban na nahiyoyi.
Sauran guda 769 kuma an lissafa su ne kawai a matsayin “yan take baya”, saboda saboda ba su cika sharuɗɗan da alƙalan THE ke buƙata ba.
Jami’o’in Najeriya ba su taɓuka ƙoƙari ba a wannan shekara, domin a shekarar da ta gabata, University of Ibadan da University of Lagos sun zo a tsakanin na 401 zuwa na 500. Ita kuma Covenant University ta zo tsakanin ta 601 zuwa ta 800.
Haka a shekarar da ta gabata jami’o’in 9 ne suka samu shiga daga Najeriya, amma a wannan shekara 7 ne kaɗai.
University of Oxford ce ta zo ta 1 a duniya, wadda ke Ingila. Dama kusan shekaru goma kenan duk shekara ita ke zuwa ta 1. Sai Stanford University ta Amurka ta zo ta 2, bayan da ita ce ta 4 a shekarar da ta gabata.
Massachusetts University of Technology da ke Amurka ce ta 3, bayan da ta zo ta 5 a shekarar da ta gabata.
Ita kuwa Harvard University da ke Amurka, ta 4, bayan da ita ce ta biyu a shekarar da ta gabata.
University of Cambridge ta zo ta 5, yayin da a shekarar da ta gabata ita ce ta 3.
Discussion about this post