Majalisar Dattawa ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake ta yaɗawa cewa ana ƙulle-ƙullen tsige Sanata Godswill Akpabio daga kan kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu ya fitar ranar Asabar a Abuja, ya ce rahoton da wata jarida ta buga cewa wasu sanatoci sun haɗu a Saudi Arabiya, su na shirya tuggu da ƙulle-ƙullen tsige Akpabio, ƙarya ce.
Zargin shirye-shiryen tsige Akpabio, wanda aka ya zama Shugaban Majalisar Dattawa a ranar 13 Ga Yuni, sai ƙara ƙarfi ya ke yi tun a cikin watan da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, wato watan Yuni kenan.
An ce wasu na ganin Akpabio ɗan-amshin-Shata zai zama a hannun Fadar Shugaban Ƙasa.
Sai dai kuma an rasa samun ko da sanata guda ɗaya da ya iya fitowa ya ce tabbas su na ƙulle-ƙullen tsige Akpabio.
Adaramodu ya ce kawunan ‘yan Majalisar Dattawa a haɗe ya ke. “Don haka maganar a ce za a tsige shugaban majalisa ba abu mai yiwuwa ba ne.
Ya ce kalaman da aka watsa a wasu kafafen yaɗa labarai suka watsa, labari ne da ke cike da ƙarairayi, kuma ayoyin Shaiɗan ne wasu Shaiɗanu su ka watsa, domin su watsa shaiɗanci a cikin ƙasar nan.
Zagin ya zo daidai lokacin da ‘Yan Majalisa su ce duk wanda ya ƙara cewa an ba su naira miliyan ɗari-ɗari kuɗin tallafi, sai sun maka shi kotu.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa sun ƙaryata zargin cewa an yi masu watandar Naira miliyan 100 ga kowanen su, a matsayin kuɗin tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa, bayan cire tallafin fetur.
Kakakin Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce rahoton da ake yaɗawa wai an yi masu kasafin Naira miliyan 100 ga kowanen su, ƙarya ce tantagaryar ta.
Lamarin ya samo asali ne daga wani rahoto da aka watsa a ranar Alhamis cewa Mataimakin Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC, Christopher Onyeka, ya ce an raba wa kowane sanata Naira miliyan 100, a matsayin kuɗaɗen tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa bayan cire tallafin fetur, “alhali an raba wa ‘yan Najeriya marasa galihu shinkafa da masara.”
Sanatocin Najeriya su 109, ta a bakin kakakin su, sun haƙiƙice cewa zargin wata mummunar manufa ce domin a ingiza talakawa a kan su.
“Shin waɗannan masu mugun nufin me su ke son cimmawa ne daga wannan sharri da ƙarya da suka kantara wa ‘Yan Majalisa?
“Babu wanda ya bai wa Sanatoci Naira miliyan 100 ko wani abu makamancin haka.
“Shin daga wane kasafin aka kafci kuɗaɗen aka raba mana? Wannan zargi sheɗanci daga wasu kafafen yaɗa labarai da kurbatsatstsun ‘yan siyasa domin su tozarta Sanatocin Najeriya.
Haka ita ma Majalisar Tarayya ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran su, Akin Rotimi, sun ƙaryata zargin su ma an raba wa kowanen su naira miliyan 100 a matsayin kuɗaɗen tallafi.
Adaramodu cewa ya yi Majalisar Tarayya ba za ta ɓata lokaci ba wajen gaggauta maka duk wani mai yaɗa wannan ƙarairayi a kan su.
Discussion about this post