Majalisar Tarayya dakatar wani shirin damƙa yankin Sina da ke cikin Ƙaramar Hukumar Michika ga Kamaru.
Ƙaramar Hukumar Michika na cikin Jihar Adamawa.
Shugabar Kwamitin Tantancewa da Sasanta Tankiyar Kan Iyakokin Ƙasa, Ben Lar ce ta yanke hukuncin dakatarwar a ranar Talata, lokacin zaman sauraren binciken tankiyar kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.
Lar ta ce a gaggauta dakatar da shata kan iyakar, har sai an sasanta tankiyar tukunna.
Lar ta ƙara da cewa kwamitin zai kai ziyara Jihar Adamawa, domin ya samu cikakken rahoto.
Ta ƙara da cewa tuni har sun sanar da Gwamnan Jihar Adamawa batun ziyarar da kwamitin zai kai jihar.
Kwamitin ya kuma yi ƙorafin cewa babu shingayen jami’an tsaro a kan iyakoki kuma babu barikin sojoji, musamman kan iyakokin Najeriya da Kamaru.
Lar ta ce wannan ya tilasta aka yi zaman tattaunawa tsakanin kwamitin da jami’an tsaro na ɓangarori daban-daban, domin ganin an inganta matakan tsare kan iyakokin Najeriya baki ɗaya.
Shi kuwa Daraktan Hukumar Kula da Kan Iyakoki ta Ƙasa, Adamu Adaji, ya shaida wa kwamitin cewa sun fara shata kan iyakar ce a bisa tsarin da Kotun Ƙasa da Ƙasa, ICJ ta gindaya.
Discussion about this post