Kwamitin Majalisar Tarayya ta fara binciken yadda NNPCL ya sayar da gidajen mai har 550, ga kamfanin OVH Energy.
CIkin wata wasiƙa da ke ɗauke da sa ranar 28 ga Agusta, Kwamitin Majalisa ya aika wa Daraktan Kula da Gidajen Man NNPCL, Hassan Nalaraba.
Wasiƙar ta tunatar da shi cewa “ka na sane cewa ranar 28 ga Yuli, Majalisa ta karanto wani hanzarin binciken abubuwan rashin daidai da aka tafka da kuma zargin harƙalla a NNPC Retail.
“Kan haka Majalisa ta kafa kwamitin binciken zargin badaƙala”
Kan haka ne aka gayyaci NNPCL ya gabatar da satidiket na rajistar OBH, Nueoil da NRL, wato mai kula da gidajen man NNPCL.
An kuma buƙaci su gabatar da kwafen dukkan hada-hadar kuɗaɗen NNPCL, OBH da Nueoil daga 2015 zuwa yau.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin abin da kwamitin ya buƙata.
Kwamiti ya nemi a gabatar da bayanan a cikin maɓallin ‘flash drive’ a ofis mai lamba 0.09 a Majalisar Tarayya, a ranar Laraba, kuma kada a wuce ƙarfe 12 na rana, 30 Ga Agusta.
Babu tabbaci ko alamun NNPLC ya aika da bayanan, musamman tunda dama a asirce aka yi cinikin.
PREMIUM TIMES ta buga labarin Majalisar Tarayya ta umarci NNPCL ta soke cefanar da gidajen mai 550 na NNPCL ga Kamfanin OVH.
A zaman Majalisar
Tarayya a ranar Alhamis, 28 ga Agusta ne ta umarci NNPCL ta soke cefanar da gidajen mai 550 na NNPC ga Kamfanin OVH.
Sannan kuma ta ce a binciki yadda aka yi harƙallar cefanar da su a asirce.
Lamarin ya taso daga wani ƙorafi da Miram Onuoha ta gabatar, wata ɗaya bayan PREMIUM TIMES ta fallasa harƙallar.
Harƙalla Da Gidogar Sayar Da Gidajen Mai Na NNPCL A Asirce:
Yadda aka sayar da Gidajen Man NNPC 550 ga Oando, kamfanin man su Tinubu a asirce:
Labari ne na wata gagarimar harƙallar da a tarihin Najeriya ba a taɓa yin kamar ta a NNPC ba.
Labari ne mai tsawo kamar zaren kurkunu, wanda tilas sai dai mu taƙaita kawai.
Kowa ya sani daga yau cewa tun a ranar 1 Ga Oktoba, 2022, duk inda mai karatu ya ga Gidan Man NNPC, to rufa-rufa kawai, mallakar Oando ne, a asirce ko a fakaice.
Dalla-dalla:
Wala-wala Da Gada-gadar Sayar Wa Oando Gidajen Man NNPC 550 A Asirce:
1. Da farko an yi wa ‘yan Najeriya rufa-rufar cewa Sashen Rukunin Gidajen Man NNPC ya saye Gidajen Mai 388 na Kamfanin OVH. Wato idan aka haɗa da gidajen mai 550 na NNPCL, za su zama 938 kenan.
To, ‘yan Najeriya ba su sani ba ashe gidajen mai 550 na NNPC ne aka sayar wa Kamfanin OVH.
2. Kamfanin OVH dai Oando ne ya yi kura-da-fatar-akuya. A ranar 30 Ga Yuni, 2015 Oando ya rikito ƙarin jarin Dala Miliyan 210, inda ya haɗiye kamfanin HN da na ‘Vitol’, ya sauya suna zuwa OVH.
3. Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya naɗa tsohon jami’in OVH Energy mai suna Hubb Stocsman Shugaban Gidajen Mai na NNPC.
4. Kuma Mele Kyari ya naɗa tsohon Shugaban Gudanarwar OVH, Mumuni Dangazau, Mashawarcin Musamman na sa.
5. Daga nan sai Mele Kyari ya yi watsi da Babban Mataimakin sa, aka daina komai da shi, Kyari ya rungumi Stocksman da Dangazau.
6. Wannan ciniki dai tamkar matacce ne ya sayi rayayye, domin a lokacin, Oando ba ya samun riba a hada-hadar fetur da gas a Afrika.
7. Daga nan sai ya kasance babu ma’aikacin NNPC ko ɗaya a NNPC Retail, wato Sashen Rukunin Gidajen Man NNPC. Saboda 9 daga cikin su 12, duk daga OVH aka ɗauko su.
8. Cikin watan Yuni, 2023 sai Stocksman ya tara ma’aikatan NNPC Retail, ya ce masu za a maida Hedikwatar NNPC Retail zuwa Legas, wato inda Hedikwatar OVH ta ke kenan.
9. A ranar ce dukkan ma’aikatan su ka gane dai OVH, wato su Oando ne su ka sayi gidajen man NNPC 550, ba NNPC ne ya sayi gidajen man Oando 338 ba.
10. Dama kuma PREMIUM TIMES ta gano ashe gidajen man OVH 94 kaɗai, 100 jingina ce, sauran kuma duk na wasu ne daban.
Discussion about this post