Shugaban kungiyar likitocin hakora na Najeriya NAPD Ify Adegbulugbe ta bayyana cewa Kwararrun likitocin hakoran 84 ne kacal ake da su a kasar nan.
Likitan da bayyana haka ne da take ganawa da manema labarai ranar Lahadi.
Adegbulugbe ta ce karancin likitocin hakora da ake fama da shi a Najeriya na da nasaba da yadda jami’an lafiya ke ficewa daga kasar nan zuwa kasashen waje.
Likitar ta kuma ce tsadar kiwon lafiya na daga cikin matsalolin da ake fama da shi a kasar nan.
Ta ce tsadar farashin kayan aiki na daga cikin matsalolin da ake fama da shi.
“Da dama kan yi amfani da dabarun gargajiya wasu Kuma sai tura ya Kai bango sannan ake zuwa asibiti.
” Inda aka fi samun matsala shine wajen kula da yara kanana da ke fama da ciwon hakora. Karancin likitoci na sa a rika shiga cikin mawuyacin hali.
Akwai ‘yan Najeriya sama da mutum miliyan 200, babu yadda za a ce wai kwararrun likitoci sama da 84 kacal su iya kula da mutane irin haka.
Discussion about this post