Kungiyar likitocin Najeriya MDCAN ta bayyana cewa kwararrun likitoci da malaman dake koyar da aikin likitanci sama da 500 sun fice daga kasar nan zuwa kasashen waje.
Sabon Shugaban kungiyar Mohammad Aminu Mohammad ya sanar da haka a taron BDM da kungiyar ta shirya wanda aka fara daga ranar 4 zuwa 20 ga Satumba a jihar Kano.
Mohammed ya ce likitocin na ficewa daga kasar nan saboda rashin inganta fannin lafiya da walwalan ma’aikatan lafiya da gwamnati ta kasa yi.
Ya kuma ce yawan ficewa daga kasar da jami’an lafiya ke yi ya shafi ingancin ilimin da dalibai a fannin lafiya ke samu.
“Rashin maida hankali wajen inganta fannin lafiyar kasar nan na daga cikin matsalolin dake sa ma’aikatan lafiya shiga yajin aiki.
“MDCAN ba ta da iko hana wani ko wata jami’ar lafiya ficewa daga kasar saboda yin hakan tauye hakkin su.
Mohammed ya yi kira gwamnati da ta yi gaggawar daukan mataki domin ceto rayukka da tattalin arzikin kasar na ta hanyar inganta fannin kiwon lafiya a kasar da kuma daɗɗa wa likitoci da ma’aikatan asibiti.
Discussion about this post