Wani jigo a jam’iyyar NNPP a yankin Kudu Maso Yamma, Alhaji Abbas ya shaida wa jaridar PUNCH cewa Rabiu Kwankwaso ya yi sanadiyyar faɗuwar NNPP a shari’ar zaɓen gwamnan Kano.
Idan ba a manta ba kotu ta kwaxe kujerar gwamnan Kano daga hannun Abba Yusuf na NNPP, ta bayyana cewa Nasiru Gawuna na APC ne ya yi nasara a zaɓen.
Kotu ta ce an shigar da haramtattun kuri’u har 163,000 wanda ba saka musu tambarin hukumar zaɓe ba da kuma sa hannun hukumar
Hakan yasa da aka zaftare waɗannan kuri’u sau Gawuna na APC ya fi yawan kuri’un da aka kada wa Abba Yusuf.
Sai dai kuma Abbas ya zargi tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Kwankwaso cewa shine ya yi sanadiyyar faduwar Jam’iyyar a shari’ar Kano.
” Tunda Kwankwaso ya koma ya rungumi APC, yana ta bibiyar ta don a yi masa minista na san za a rina. Ya saida jam’iyyar don neman kujerar siyasa. Wannan shine kawai abin da ya faru. A dalilin haka ne APC suka gano yadda za su bi a Shari’ar su yi nasara.
” Jam’iyyar ta hango haka da wuri, ya sa ta gaggauta fatattakar sa daga NNPP. Saboda maimakon ya maida hankali wajen gina jam’iyyar da bin ƙa’idojin ta ya ɓige ne da neman kujerar siyasa a hannun jam’iyya mai mulki.
“Sannan kuma ya tsaya ma a yi abinda ya dace wurin zaɓen ƴan takara yadda yakamata, ya yi wa mutane rufarufa, ga shi yanzu abin ya rufta da kowa.
Discussion about this post