Kwamitin Amintattun jam’iyyar NNPP sun kori jagoran tafiyar Kwankwasiyya na kasa, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar Kwatakwata.
Hakan ya fito ne daga wata sanarwa wanda Alhaji Abdulsalam Abdulrasaq, ya saka wa hannu.
“Tsarin mulkin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) 2022 (Kamar yadda aka gyara) shine kundin tsarin mulkin jam’iyyar kuma ba a amince da gyaran kundin tsarin mulki ba sai bayan babban zaben 2027.
Korar Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta tabbata yau kuma an rattaba hannu akan haka.
“ Sannan kuma an amince da murabus din Dakta Boniface Okechukwu Aniebonam a matsayin shugaban BoT na jam’iyyar yayin taron kwamitin karshe na ranar 29 ga watan Agusta 2023.
“ Haka kuma an amince da zaben Temitope Aluko a matsayin Shugaban BoT da Engr. Babayo Mohammed Abdullahi a matsayin Sakataren Hukumar, a ranar 29 ga Agusta, 2023.
Don haka BoT na jam’iyyar NNPP ya bukaci jama’a da su yi watsi da taron manema labarai kungiyar Kwankwasiyya, karkashin jagorancin Kwankwaso su ka yi da babatun da suka rika yi.
Ba yan haka kuma NNPP ta ce kungiyar Kwankwasiyya ba jam’iyya ba ce a Najeriya.
A karshe jam’iyyar ta ce tana duba sakamakon shari’ar kotun zaben gwamnan Kano, za ta kuma garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun.
Discussion about this post